An kashe mutane 45 a Birnin Gwari

Babban Sipeton 'yan sandan Nigeria ya yi alkawari tura karin yan sanda yankin Birnin GwariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBabban Sipeton ‘yan sandan Nigeria ya yi alkawari tura karin yan sanda yankin Birnin Gwari

Rahotanni daga karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 45 a kauyen Gwaska da ke yankin.

Lamarin dai ya faru ne kasa da mako guda bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Janruwa inda suka kashe wasu masu aikin hakar ma’adinai da dama.

‘Yan bindigan wadanda ake kyautata zaton sun fito ne daga wasu dazuzzuka na jihar Zamfara sun kone kusan daukacin gidajen da ke kauyen Gwaska da kuma kauyen Kuiga.

Wani dan asalin yankin Zubairu Abdurrauf, Dan masanin Birnin Gwari ya shaida wa BBC cewa akasarin wadanda aka kashe ‘yan sakai ne da ke kokarin kare garuruwansu daga hare haren ‘yan bindigan da suka addabi al’umma.

A lokacin da ya ziyarci yankin a ‘yan kwanakin nan, babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya yi alkawarin tura karin ‘yan sanda yankin na Birnin Gwari.

A ‘yan shekarun nan dai ana samun tashin hankali da kashe-kashen jama’a a jihar Kaduna da ma wadansu jihohi makwabta.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *