An haramta hadawa da shigar da kodin Najeriya

Reports
Man pouring cough syrup into a bottle

Najeriya ta haramta hadawa da sayar da maganin tari mai Kodin bayan BBC ta bankado yadda ake sayar da shi barkatai.

Ministan Lafiya na kasar Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun Mataimakin Daraktan watsa Labara na Ma’aikatar Olajide Oshundun.

Mr Oshundun ya shaida wa BBC cewa za a ci gaba da sayar da wadanda suka rage amma kawai ga wadanda likitoci suka ce a bai wa.

A binciken da BBC ta gunadar ya gano cewar masu safarar kodin suna aiki cikin kamfanonin da ke hada maganin, kuma suna sayar da magungunan ba bisa ka’ida ba.

Miliyoyin matasa a Najeriya na shan maganin, wanda ke sa mutum ya nace masa, domin su bugu.

Maimakon amfani da kodin, ministan ya ce masu hada maganin tari su rinka amfani da Dextromethorphan wanda bai kai kodin illa ba.

Ministan ya kuma umarci Hukumar Kula da Masu Hada Magunguna ta Najeriya, (PCN) da kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) da su sa ido wajen janye kodin din dake cikin kasar.

Za a yi haka ne domin tabbatar da yawansu da kuma sanya musu alama, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce ministan ya umarci hukumar PCN ta cigaba da tabbtar da cewa an bi dokar hana hadawa da kuma shigowa da kodin cikin kasar.

Minsitan ya ce ma’aikatarsa za ta tabbatar da cewa hukumomin NAFDAC da PCN, da NDLEA mai yaki da miyagun kwayoyi sun yi aiki tare domin tabbatar da cewa na bi dokokin da aka kafa kan amfani da kodin a Najeriya.

Alkaluman hukumomi sun bayyana cewa kimanin kwalbar kodin miliyan uku ake sha a kowacce rana a jihohin Kano da Jigawa kawai.

Da ma can doka ta haramta sayar da kodin a Najeriya sai ga wanda likita ya bai wa izini, amma BBC ta gano yadda ake hada baki da wasu masu kamfanonin hada magunguna da ‘yan kasuwa wurin sayar da shi ba bisa ka’ida ba.

Wani wakilin BBC a Abuja ya ce babu tabbas kan tasiri ko akasin haka na wannan sanarwa da ministan ya bayar, ganin yadda saba doka da cin hanci suka zama ruwan dare a Najeriya.

Presentational grey line

Martani kan rahoton BBC

Ba ya ga sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar na haramta hadawa da shiga da kodin kasar, biyo bayan rahoton na BBC, wasu masu fada-aji na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan batun:

 • Shugaban Majalisar Dattawa ta kasar Dr Abuabakar Bukola Saraki ya yabawa BBC kan rahoton da ta yi
 • Ya ce hakan ya nuna cewa akwai bukatar kasar ta dauki matsalar shan miyagun kwayoyi da matukar muhimmanci
 • Uwar gidan Shugaban kasar Hajiya Aisha Buhari ta nuna matukar damuwarta kan yadda matasa ke ta’ammali da kwayoyi bayan rahoton na BBC
 • Kamfanin Emzor pharmaceutical ya dakatar da sayar da maganin mai dauke da kodin.
 • Kamfanin ya kuma kori jami’in cinikinsa wanda aka nuna yana sayar da kodin ga wakilin BBC

Aisha Buhari ta kara da cewa: “A matsayina na uwa, hakika na damu kan wannan lamari, yana da matukar muhimmanci mu tashi tsaye domin ganin ‘ya’yanmu sun daina wannan dabi’a”.

Presentational grey line

Maganin Kodin – yadda girman matsalar ta ke

Man pouring cough syrup into a bottle
 • Kodin magani ne da ke rage zafin ciwo ko na jiki amma yana cikin magungunan da ke sa maye.
 • Idan aka sha shi fiye da kima, to yana janyo tabin hankali kuma yana yin illa ga koda ko hanta ko zuciyar mutum
 • An fi hada maganin tari na kodin da lemun kwalba kuma dalibai ne suka fi shansa.
 • Daga kasashen waje ne ake shigowa da kodin, amma a cikin Na jeriya ne kamfanoni fiye da 20 suke hada magani
 • Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar na kokarin kawarda da matsalar.
 • A samamen da taka kai a baya-baya nan, ta kwato kwalaben Kodin 24,000 daga cikin wata babbar mota a jihar Katsina.
 • Ta’ammali da kodin babbar matsala ce a Afirka, inda ake samun rahotanni game da wadanda ba su iya rabuwa da shi a Kenya da Ghana da Niger da kuma Chadi

A shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta hana amfani da shi a kasar sakamakon rahoton da ta samu game da yawan masu ta’ammali da shi a matsayin kayan maye. BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *