Harin bam ya kashe mutum 24 Mubin jihar Adamawa

Taswirar Mubi

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar wa BBC cewar harin bam-bamai da aka kai wani masallaci da ke kasuwar garin Mubi ya kashe akalla mutum 24.

Wasu da dama ne kuma suka jikkata a hare-haren wadanda ‘yan kunar bakin-wake biyu suka kai.

Abin fashewa na farkon dai ya tashi ne a cikin wani masallaci da ke layin ‘yan gwanjo a kasuwar garin da misalin karfe 12.30 na rana.

Jim kadan kuma sai daya abin fashewar ya tashi a kusa da inda na farkon ya tashi.

Wani wanda ya shaida lamarin ya gaya wa BBC cewa yayin da mutane suke tserewa daga kasuwar, sun ga jami’an tsaro suna tafiya wurin.

  • Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri
  • Boko Haram: An kashe mutane a masallaci a Borno

Ya kara da cewa an yi ta kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su a cikin Keke Napep domin kaisu inda za su samu magani.

Kungiyar Boko Haram ta taba kwace iko da garin na MubiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai wannan harin kawo yanzu.

Sai dai kungiyar Boko Haram ta kan kai hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya ciki kuwa har da jihar ta Adamawa.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *