‘Yan matan Chibok 15 ne ke raye cikin 112 da ke hannun Boko Haram’

Reports
ChibokHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionHar yanzu Boko Haram na rike da ‘Yan Matan Chibok 112.

Dan jaridar nan na Najeriya da ya kware game da ba da rahotanni kan kungiyar Boko Haram Ahmed Salkida, ya ce ‘yan matan Chibok 15 kawai suka rage a raye daga cikin sama da 100 da har yanzu ke hannun kungiyar.

Salkida ya fadi haka ne a cikin jerin sakwannin da ya wallafa a shafinsa na twitter, a yayin da ake cika shekaru hudu da sace ‘yan matan.

Ana kallon Ahmad Salkida a matsayin wanda ke da kusanci da Boko Haram, kuma ya jima yana ba da rahotanni a kan ayyukan kungiyar tare da zama mai shiga tsakanin kungiyar da gwamnati a can baya.

Wani mai magana da yawun gwamnati ya shaida wa BBC cewa har yanzu suna cigaba da tattaunawa da mayakan Boko Haram domin neman a sako ‘yan matan 112.

Ya kara da cewa babu wata hujja da za ta sa su amince cewa ‘yan matan sun mutu.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar wa da BBC da wannan ikirarin na Salkida game da makomar sauran ‘yan matan na Chibok.

  • Boko Haram ta sace yara fiye da 1000 a Najeriya – UNICEF
  • Najeriya: Shekara hudu da sace ‘yan matan Chibok

A cikin bayanansa, Salkida ya ce bincikensa ya tabbatar ma sa da cewa yawancin ‘yan matan sun mutu ne saboda barin wuta da ruwan bama-bamai ta sama da kasa da jami’an tsaro ke kai wa Boko Haram.

Sannan ya ce wasu majiyoyinsa sun tabbatar ma sa da cewa ‘yan matan 15 da ke raye sun auri ‘yan Boko Haram, kuma a yanzu mazajensu ke da hakki da su.

“Sun fita daga ikon shugaban Boko Haram Abubakar Shekau” a cewar Salkida.

Ya kara da cewa tun da har sun auri wasu ‘yan Boko Haram, yanzu Shekau ba ya da hakkin tattaunawa da gwamnati game da sakinsu.

Sai dai dan jaridar bai bayyana sunayen sauran ‘yan matan 15 da ya yi ikirarin suna raye ba, yana mai cewa hakkin gwamnati ne ta yi bincike.

Ahmad Salkida, ya sha ikirarin shiga tsakani domin sakin ‘yan matan a madadin gwamnati tun zamanin gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Salkida ya ce cikin shekara 18 da ya yi yana aikin jarida, ya shafe shekara 13 ne yana bibiyar ayyukan kungiyar Boko Haram.

Jami’an tsaron Najeriya sun taba kama Salkida bayan sun yi tallar suna nemansa ruwa a jallo a 2016.

A watan Agustan 2016 ne rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi zargin Salkida da cewa yana da dangantaka da kungiyar Boko Haram.

Jami’an tsaron Najeriya sun kama shi kafin da daga bisani suka sake shi.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne mayakan Boko Haram suka shiga garin Chibok suka sace ‘yan mata 276, al’amarin da ya ja hankalin duniya.

Sai dai tun a lokacin ne wasu daga cikinsu suka tsere.

Sojojin Najeriya kuma sun ceto wasu daga cikinsu, bayan musayar wasu ‘yan Boko Haram da ke tsare a hannun jami’an tsaron kasar.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *