An cafke mai hadawa Boko Haram bama-bamai

News
Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta na samun nasarar fatattakar 'yan Boko HaramHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionRundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta na samun nasarar fatattakar ‘yan Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta sun cafke wani mutum daya shahara wajen hada bama-bamai ga mayakan kungiyar Boko Haram.

Rundunar ta ce an cafke Adamu Hassan ne da ake yiwa lakabi da suna ‘baale’ a garin Kaltungo na jihar Gombe da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar.

  • Buhari ya yi wa ‘yan Boko Haram tayin afuwa

Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce an cafke mutumin ne a wani samame da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya suka kai.

Kamfanin dillancin labaru na Nigeria ya ambato Kanar Nwachukwu na cewa dakarun sojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram uku a bata kashi da suka yi a tsaunukan Bokko Hilde da ke kan hanyar Ngoshe zuwa Pulka a jihar Borno.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *