Dino Melaye zai fitar da sabon kundin wakoki

Reports
Dino Melaye ya ce akwai gyara a jam'iyyar APC mai mulkin NajeriyaHakkin mallakar hotoFACEBOOK/DINO MELAYE

Dan majalisar dattawan Najeriya Dino Melaye ya ce nan ba da jimawa ba zai fitar da sabon kundin wakoki.

Sanatan ya shaida wa BBC cewa “kowa yana da baiwar da Allah ya yi masa. Ni Allah ya yi min baiwar waka, da a ce na je na zage ka gara na yi maka gwalo. Saboda haka ina son waka. In Shallau kwanan nan zan fitar da sabon kundin waka.”

A cewarsa, yana matukar son hawa motoci na kece-raini saboda suna burge shi.

Da yake bayar da amsa kan zargin da ake yi masa na gudanar da rayuwa harholiya, Sanata Dino ya ce “Duk wanda ya ce ba zan ji dadin rayuwata ba karya yake yi; zan rika sa kaya masu kyau, zan hau motoci masu kyau, amma ba zan yi sata ba kuma tun kafin na zama sanata nake hawa motoci. Tun da na zama sanata ban sake sayen sabbin motoci ba”.

  • Dino Melaye ya fito a wakar hip-hop

Dan majalisar dattawan ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.

Ya ce ba ya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam’iyyar da mutum ya fito indai batun gaskiyar ya kama ko dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ko kuma APC mai mulki.

”Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya.”

“A halin da ake ciki ni fa ko Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko Bukola Saraki, ko Dogara kai ko uban da ya haife ni idan ya yi ba daidai ba sai na fada, babu wanda ya isa ya hana ni fadar gaskiya sai dai a kashe ni,” in ji Dino Melaye.

Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Kogi ba ta mayar da martani ba game da batutuwan da sanatan ya zarge ta a wannan hirar ba, amma a baya ta sha musanta su.

A ranar Laraba ne rundunar `yan sandan kasar ta ayyana dan majalisar dattawan a cikin mutanen da take nema ruwa-a-jallo, bisa tuhumar da wata kotu ke masa ta taimaka wa miyagun ayyuka, zargin da ya musanta.

Kazalika akwai kalubalen da yake fuskanta na kiranye daga al`ummar mazabarsa.

Dino Melaye

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *