Fursunoni 68 sun mutu a tarzoma a Venezuela

News
Wata mata da danginta ke cikin caji ofis din na kokarin kutsawaHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionDangin wadanda ake tsare da su a caji ofis din sun yi kokarin kutsawa ciki a lokacin da ya kama da wuta

Mutane akalla 68 ne suka mutu da dama suka samu raunuka a sakamakon tarzoma da fursunoni suka tayar a wani ofishin ‘yan sanda a birnin Valencia na kasar Venezuela.

Ana ganin an samu asarar rayukan mutane da yawa ne saboda gobarar da ta tashi bayan da tsararrun suka cinna wuta a katifu a kokarin da suka yi na tserewa.

Wani jami’in gwamnati a jihar Carabobo, inda garin da lamarin ya faru yake, ya ce jihar na cikin makoki.

Dangin fursunonin sun ce da dama sun mutu ne watakila a sanadiyyar hayakin da suka shaka.

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa ‘yan uwan wadanda ke tsare a caji ofis wadanda suka kewaye wurin suna kokarin shiga ciki a lokacin da lamarin ke faruwa.

Wani jami’in gwamnati ya ce an harbi wani dan sanda, sannan ‘yan kwana-kwana sun yi nasarar kashe wutar.

Sannan ya kara da cewa likitoci masu bincike na kokarin tantance yawan mutanen da suka mutu.

Rahotannin da ba na hukumomi ba wadanda kafafen watsa labarai ke bayarwa na cewa yawan mutanen da suka mutu ya kama daga 60 zuwa 78.

Wasu daga cikin ‘yan uwan wadanda ke tsare a caji ofis din sun bayyana wa manema labarai cewa sun zaku su san ainahin abin da ya faru da kuma halin da ‘yan uwansu ke ciki.

Wata mata da danta ke tsare a wurin ta ce, ”ba su gaya min komai ba. Ina son sanin halin da dana yake ciki. Ba ni da wani bayani a kansa, ban san komai ba. Muna son bayani a kan iyalanmu. Muna bukatar bayani. Duba yadda muka zaku.”

Gidajen yari a Venezuela na fama da cunkoso da matsalar satar shiga da makamai da miyagun kwayoyi da kuma kungiyoyin bata-gari.

Kasar na fafutukar yadda za ta rika tsare fursunoninta a yayin da take fama da matsalar tattalin arziki, abin da ke sa tsare masu laifi a wurare na wucin-gadi kamar wannan caji ofis din da aka samu asarar rayuka a Valencia.

Shugaban wata kungiyar nema wa jama’a ‘yanci, Carlos Nieto ya ce wasu ofisoshin ‘yan sandan suna dauke da tsararru linki biyar na yadda ya kamata a ce an sa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.