Afrin: Siriya na dab da karbe birnin daga hannun YPG

News
Kurdawa na gudun daga birnin Afrin saboda yakiHakkin mallakar hotoAFP
Image captionKurdawa na gudun daga birnin Afrin saboda yaki

Sojojin Tukiyya tare da ‘yan tawayen Syria na dab da karbe garin daga hannun mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.

An yi wa garin wanda ke arewacin Syria kofar rago, kuma mazauna garin su kimanin 350,000 na ta ficewa ta wata hanya daya da ta rage musu kafin abinci da ruwa su kare baki daya.

Turkiyya ta ce mayakan YPG ‘yan ta’adda ne, kuma ta ce suna da alaka da ‘yan tawayen Kurdawa da suka dade suna yakin neman kafa kasarsu a cikin Turkiyya.

Amma kasashen yammacin Turai na kallonsu a matsayin abokan tafiyarsu ne a yakin da su ke yi da kungiyar IS.

Wata mata mai suna Ranya na daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su a garin na Afrin:

“Jiya da rana an rika kai hari kan motocin da ke makare da mutanen da ke kokarin tserewa daga yakin. Ko ina ka duba sai gawarwaki, kuma cikin dare jiragen yaki sun kai wa asibitin Afrin hari.”

Syria

Kungiyar YPG da wata kungiyar masu sa ido sun ce wani harin jirgin yaki da Turkiyya ta kai a kan asibitin ya halaka fararen hula 16.

Amma Turkiyya ta musanta tuhumar da ake mata, kuma ta fitar da wani bidiyo da ke nuna cewa asibitin na nan kalau.

Majalisar Turai da ministan harkokin waje na Faransa sun nemi Turkiyya da ta dakatar da wannan yunkurin sojin na karbe garin da ta ke yi.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *