An gano maganin cutar Kanjamau da zai iya warkar da ita

News

Wasu likitoci a asibitin ‘Beth Israel Massachusetts’ dake kasar Amurka sun gano maganin cutar Kanjamau ‘antiretroviral therapy (ART)’ da ke iya warkar da mara lafiya kwata-kwata daga cutar.

Likitocin sun bayyana cewa maganin na hana kwayoyin cutar hayayyafa a jikin mutum har na tsawon watannin shida.

Binciken ya nuna cewa lallai fa idan mai dauke da cutar ya dage da shan maganin zai iya warkewa tatas daga cutar.

Shugaban wadannan likitoci Dan Barouch ya yi karin bayani cewa sun gano haka ne bayan binciken da suka gudanar a jikin wasu birai 44.

” Bayan mun tabbatar wadannan birai na dauke da cutar Kanjamau sai muka fara basu wannan magani, bayan makonnin 96 sai muka ga cewa kwayoyin cutar bai hayayyafa ba tun bayan lokacin da muka fara basu maganin. Hakan ya nuna cewa cutar bai ci gaba da yi wa garkuwar jikin birai lahani ba.”

” Daga nan sai muka raba su zuwa gida biyu inda rabi muka ci gaba da basu tsohon maganin cutar Kanjamau sannan rabin muka ci gaba da basu sabon maganin na tsawon makonin 16.”

Dan Barouch ya ce sakamakon da suka samu ya nuna cewa kwayoyin cutar ya kara yawa a jikin kashin biran da suka yi amfani da maganin da ake amfani da shi a da, kashin da aka basu sabon maganin kuwa, ba a ga kwayoyin cutar a jikin su kwata-kwata.

@hausa.premiumtimesng.com

Leave a Reply

Your email address will not be published.