An yi hatsaniyar addini a Kaduna

News
KadunaHakkin mallakar hotoKADUNA STATE GOVERNMENT
Image captionGwamnatin Kaduna ta kaddamar da bincike kan rikicin Kasuwar Magani

An kona gidaje bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Babu dai wani cikakken bayani game da dalilin faruwar rikicin amma wasu rahotanni sun ce rikici ne tsakanin mabiya addinin kirista da musulmi.

Rahotannin da muka samu sun ce, sabani na soyayya tsakanin wata budurwa kirista da musulmi ne ya tayar rikicin tun a ranar Laraba, inda kiristoci suka bukaci duk wata da ke son musulmi ta daina.

Kuma Kiristocin sun bukaci duk macen da ta yi aure a gidan musulmi ta fita ko su fitar da ita da karfi.

A yau litinin kuma wasu matasa sun fantsama cikin gari inda rikici ya kaure.

‘Yan sanda ba su bayyana mutanen da suka rasu ba, amma hausawa mazauna garin sun ce sun kirga gawarwakin mutanen 12 yayin da suka ce ana ci gaba da tattara gawarwakin wadanda suka mutu.

  • Me ya sa El-Rufai ya rusawa Hunkuyi gida a Kaduna?
  • Nigeria: Zaki ya kashe mai kula da shi a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da al’amarin, inda ta bayyana cewa ta tura jami’an tsaro domin magance rikicin da ruruwarsa.

Sai dai a cikin sanarwar da Samuel Aruwan kakakin gwamnan Jihar Kaduna ya fitar bai fadi adadin mutanen da suka mutu ba da adadin wadanda suka jikkata.

Sanarwar ta ce gwamnan Jihar Malam Nasir El Rufa’i ya umurci jami’an tsaro su gudanar da bincike tare da kame duk wadanda ke da hannu a rikicin da ya faru a Kasuwar Magani.

Tazarar nisan kilomita 31 ne tsakanin Garin Kasuwan Magani da birnin Kaduna.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.