Olympics: ‘Yan wasa da za su yi fice!

Politics
winter olympic ringsHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

An fara gasar Olympics ta 2018 a birnin PyeongChang da ke kasar Koriya ta Kudu.

Dubban ‘yan wasa daga kasashe daban-daban na duniya za su fafata a wasanni fiye da 100 da ke rukunin wasanni 15.

Ga wasu daga cikinsu da muke ganin za su haska a wannan babban biki na 2018!

Shahararrun ‘yan wasa

Yuzuru Hanyu

Yuzuru HanyuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Masu sha’awar wasan Ice skating da ake yi bisa kankara za su yaba da wannan dan wasan.

Shekaru hudu da suka gabata ne Yuzuru Hanyu ya zama dan kasar Japan namiji na farko da ya taba lashe lambar zinare a gasar Olympics na yanayin sanyi.

A lokacin yana dan shekara 19 da haihuwa, wato shi ne mutum mafi kankantar shekaru tun 1948!

Yuzuru ya kuma kasance dan wasan skating na kankara da ya fara wuce maki 100 a wasan a duniya, inda ya hada maki 101.45.

A takaice ya yi nasarar kafa matsayi 12 daban-daban!

Chloe Kim

Wannan ‘yar Amurkar mai wasan Snowboard ‘yar shekara 17 ce da haihuwa, amma tana cikin wadanda ake sa ran za su lashe lambar zinare a gasar ta bana.

Chloe KimHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Wasan da za ta fafata a kai shi ne na halfpipe, wanda dan wasan ke sudadowa akan snowboard yana sauyawa daga gefen hagu zuwa dama.

Chloe won the halfpipe and slopestyle gold medals in the 2016 Winter Youth Games.

Chloe ce t alashe lambar zinare a gasar halfpipe da slopestyle da aka yi a gasar yanayin sanyi na 2016.

Wannan ce gasar Olympics din ta ta farko, domin shekarunta sun yi kankanta a lokacin waccan gasar ta 2014.

Iyayenta ‘yan kasar Koriya ta Kudu ne, saboda haka ana sa ran za ta sami magoya baya daga Amurka da Koriya ta Kudu.

Laura Dahlmeier

An lakaba mata sunan Sarauniyar harbi a kan kankara! Gasar da za ta fafata a ciki ta harbi ce da kuma gudu kan dusar kankara.

sHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Ana sa ran Laura za ta kasance cikin taurarin da za su haska a gasar da za a yi a PyeongChang a bana.

A bara ita ce ta kasance lamba 1 a duniya!

A 2017 ta zama ‘yar wasa ta farko da ta taba lashe lambar zinare a gasar duniya daya! Babu namiji ko mace a duniya da suka taba cimma wannan matakin.

A wannan gasar ta Olympics, za ta fafata a duka wasanni shida da ake da su a gasar harbi da gasar gudun dusar kankara.

Idan ta cigaba da kokarin da aka san ta da shi a shekarun baya, da wuya a sami ‘yan wasan da za su cimmata.

Taurarin Birtaniya

Elise Christie

Elise Christie ‘yar Birtaniya ce wadda ta yi fice a gasar gudu a kan kankara. ‘Yar asalin Scotland din ce ke rike da kambun wasan gudu na mita 500 a duniya a halin yanzu.

sHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Ita ce kuma mace ta farko daga Birtaniya da ta fara lashe lambar zinare a gasar duniya!

An hana ta halartar waccan gasar ta Olympics a 2014, amma a bana ta dawo da karfinta!

Sau daya Birtaniya ta taba cin lambar zinare a wasan tsere na gajeren zango a bisa kankara. Elise na da yakini za ta sauya wannan lamarin a bana!

Katie Ormerod

Daya daga cikin wasanni mafi kayatarwa a gasar Olympics na bana shi ne na Snowboard da ake sudadowa daga saman dutse akan wani faifai a guje, kana sai dan wasan ya tashi sama yana jujjuyawa.

sHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Katie ma ‘yar Birtaniya ce, wadda ta kasance ‘yar kasar da ta zama zakara a rukunnai biyu da wasan a 2012.

It ce kuma ‘yar wasa mafi kankantar shekaru a kasar da ta taba wulwulawa sau biyu da baya a lokacin tana ‘yar shekara 15 da haihuwa.

Wannan ne gasar Olympics din ta na farko amma ta riga ta saba da lashe wasanni a kasashe kamar Kanada da Jamus da Italiya da kuma Rasha.

‘Yan wasa na musamman

‘Yan wasan tseren Bobsleigh daga Najeriya

Nigeria's bobsled teamHakkin mallakar hotoBSFNIGERIA

Wadannan fuskoki masu murmushi na wasu ‘yan wasan tseren bobsleigh da ake yi a kan dusar kankara ne daga Najeriya.

Su ne ‘yan wasa na farko da suka taba cancanta su wakilci wata kasa daga nahiyar Afirka a wannan wasan. Kuma dukkansu ‘yan Najeriya ne.

Su ne kuma ‘yan wasa na farko da suka cancanci zuwa gasar Olympics daga nahiyar ta Afirka a wasan bobsleigh.

Daga hagu ga Seun Adigun, wadda ita ce mai tuka bobsleigh din, sai Ngozi Onwumere da Akuoma Omeoga wadanda za su rika taka birkin na’urar.

Kafin wannan gasar ta bana, Seun tana yi wa Najeriya wasan famfalaki ne, inda har ta taba yin tseren mita 100 a gasar Olympics na Landan da aka yi a 2012.

Sauran ‘yan matan ma sun yi wa Najeriya wasanni daban-daban a baya.

Akwasi Frimpong and Anthony Watson

Ban da ‘yan wasa daga Najeriya, akwai wasu ‘yan Afirka da su ma za su fafata a gasar ta bana.

dHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Wadannan ‘yan wasan biyu ma za su kasance na farko da za su wakilci kasashensu.

Akwasi (wanda ke kasa) shi ne dan Ghana na biyu da zai wakilci kasarsa a gasar Olympics, kuma shi ne dan Afirka namiji daya tilo daga nahiyar Afirka da zai shiga gasar Olympics na bana.

Anthony Watson kuwa (wanda ke sama) shi ne dan kasar Jamaica na farko da zai fafata a gasar Olympics na yanayin sanyi.

Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu sun hade!

Kowa ya san cewa Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ba sa ga maciji da juna.

Sarah Murray, head coach of the combined women's ice hockey team, is seen as the North Korean women's ice hockey players arrive at South Korea's national training centre in Jinchoen on 25 January 2018Hakkin mallakar hotoREUTERS

Amma duk da rashin jituwar da ke tsakaninsu, Koriya ta Arewa ta shiga yarjejeniya da Koriya ta Kudu domin su hada kungiya daya da za ta fafata a wasan kwallon gora na kankara.

‘Yan wasa 12 daga Koriya ta Arewa da ‘yan wasa 23 daga Koriya ta Kudu sun hada kungiya daya ta mata da za ta fafata a wasannin kwallon gora na kankara.

Koriya ta Arewa na da jimillar ‘yan wasa 22 ne gaba daya! Kuma su ne za su wakilci kasar a dukkan wasannin da kasar ta shiga.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.