Talauci ya sa wata mace sayar da ruwan nononta

News
Woman kneels on street in China, breastfeeding a baby. The sign beside her has a picture of her ill baby and writing in Chinese characters. There are two plastic bags apparently filled with breast milk in the foreground.Hakkin mallakar hotoPEAR VIDEO

Wata matashiyar mata a China na sayar da ruwan nononta a kan titunan kasar da zummar tara kudin da za a yi wa ‘yarta maras lafiya magani.

Wani bidiyo da kamfanin Pear Video ya wallafa a shafin intanet na Miaopai ya nuna matar da mijinta na yin jawabin cewa suna bukatar tara akalla £11,250 domin yi wa ‘yarsu, wacce ke kwance rai kwakwai mutu kwakwai, magani.

An kalli bidiyon fiye da sau miliyan biyu da dubu 400 sanna fiye da mutum 5,000 suka yi tsokaci a kansa a shafin sada zumunta na Sina Weibo.

An dauki bidiyon ne a wurin shakatawa na yara da ke birnin Shenzhen.

Matar ta ce tana sayar da ruwan nonon nata ne domin tara kudin cikin gaggawa, saboda daya daga cikin ‘ya’yanta ‘yan biyu na kwance rai hannun Allah a asibiti.

Mijin matar ya ce asibitin na bin su bashin “dubban daruruwan kudin yuan” kuma “likitoci sun ce sai sun biya su akalla £11,250 da zarar yarinyar ta ji sauki”.

The couple with bowed heads beg passers-by for moneyHakkin mallakar hotoPEAR VIDEO

Jama’a sun kwashe shekara da shekaru suna sukar tsarin kiwon lafiyar China a yayin da mutane suka yi wa asibitocin kasar yawa sannan ana zargin cewa wasu mutanen na ba da cin hanci domin samun kulawar gaggawa.

Akasarin mutanen da suka yi tsokaci a shafukan zumunta kan batun sun bayyana jin tausayinsu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *