YADDA MUKE GWAGWARMAYAR KARE HAKKIN MATA DA YARA A NEJA — BARISTA MARYAM KOLO

Reports

ABDULRAZAK YAHUZA JERE

Masu karatu a wannan makon muna tafe maku da hira wacce ta dan shabamban da wadanda suka gabace ta. Barista Maryam Haruna Kolo, Mace ce wacce ta kai wata makura a karatun Boko da kuma rayuwar iyalai. Shahararriyar Lauya, wacce ta yi fice a bangaren kare hakkin Mata da Yara kanana,  Babbar Darakta a Hukumar kare hakkin Mata da Yara kanana.

A zantawar da ta yi da Editan Leadership A Yau, ABDULRAZAK YAHUZA JERE, ta yi shimfida kan turbar da ta ce ga shimfida rayuwar iyalai mai kyau, sannan ta kawo hanyoyin da ‘ya’ya mata za su cimma burinsu na rayuwa cikin sutura da mutunci. Har ila yau, da yake ta Alkali ce, ta bayyana shari’ar da ta taba yi wadda har yau abin yana yawo a cikin kwakwalwarta. Domin jin sauran bayanai sai a karanta hirar duka. A sha karatu lafiya: Da farko za mu so ki gabatar wa masu karatu da cikakken sunanki?

Sunana Barista Maryam Haruna Kolo, Darakta Janaral na ‘Tras Right Agency,’ a nan Minna, Jihar Neja. Da yake har kin kama aiki a matsayin ki na Darakta Janaral, za mu so ki bayyana ma masu karatu takaitaccan tarihinki. An haife ni a garin Jos, kuma na girma a cikin garin Jos, bayan haihuwana Mahaifiyata ta rasu, sai na girma a hannun Babana da ni da Yayyuna da kuma kannaina. Na fara Makarantan Firamare a Jos, wacce ake kira Fatima Primary, na gama, har ila yau na ci gaba da ‘Fati High School’ a nan Jos din, da na gama sai na koma Kano na shiga Jami’a, na yi ‘Law School’ sai kuma na yi NLD di na. Na karanta Digiri di na a Law, na je Legas na yi NLD, a ‘Nigerian Law School. Sai na dawo na yi bautan kasa a nan Minna, na kuma samu aiki a wata Chamber, sai na koma zuwa aikin alkalanci shekaru 18 kafin aka zo aka ba ni wannan matsayin na Darakta mai kula da yara.

Kin taka matakai da yawa na karatu, wannan shafi na Adon Gari, an yi shi ne don Mata,  misali yanzu idan aka samu Yarinyar da take so ta zama Barista irin ki, wace shawara za ki ba ta a kan yadda za ta samu nasara? Shawaran da zan ba ta guda daya ce, duk abin da kake yi, idan ka sa rai cewa ga abin da za ka zama sai ka fara aiki domin ka zama wannan abin, idan kana so ka zama Lauya, Lauya ba aikin da za ka ce kana zuwa kana karantawa ba tare da natsuwa ba ne, domin akalla dole sai ka natsu sosai ka yi karatu kuma shi ne ka iya ka san ka samu abin da kake nema, kuma ka cimma burin ka. Wannan ki na magana a kan mayar da hankali kenan, toh ta bangaran abin da ya shafi mu’amala musamman wasu suna ganin sau tari sukan je da niyyan karatu a makaranta , amma sai a samu rinjayar mutanan da ake haduwa da su, toh ta wannan fuskan me za ki gaya masu domin su yi rigakafi?

Abin da zan gaya ma yaro, dole ne ka natsu ka ga abin da kake so, domin idan ka ce za ka biye ma abokanai a lokacin makaranta, a kowace Jami’a za ka iya samun wasu ba ma karatun suka zo ba, kawai zuwa suke domin su bata wasu domin duk su zama kamar su. Karya kawai suke yi suna zama a makarantar, suna neman mutane  da yawa su hadu cikin su domin a lalace gaba daya. Amma in kai kasan cewa kai fa karatu ya kawo ka, ka yi fa tunani har ila yau iyayen nan naka suna kallon ka kuma suna duba ne me wannan yaron zai zama, sannan ana kwadayin cewa ya gyara rayuwar shi. Yanzu abin da muke ciki a duniya idan ba ka da ilimi, yana da wuya ka ce ka ci gaba a kowane fanni. Balantana, ita ‘ya mace, kar ku je kuna saka kanku kuna shaye-shaye ko ku je kuna zuwa wajen fati ko a je ana saka kaya kullum, ba abin da ya kai ka makaranta ba kenan, duk wannan idan aka gama a lokacin da ka fara aiki lokacin ne za ka samu wadataccan kudin da za ka iya yin duk wannan ba tare da ka yi wata wahala ba. Dole a natsu a makarantan nan kuma a cire ido daga wannan yaran da ba su da tarbiya, kuma kowa ya san yaran da ba su da kirki ai, tun da hankalinsu baya wajan karatu sai dai aje ayi wasa, aje cikin gari ayi shaye-shaye. Sai ka fita daga gefen su, sai ka yi abin da ya kawo ka makaranta, sannan kuma a hada da addu’a.

Wasu da dama za su iya cewa, ba su san dadin aikin Lauya ba, a takaice Barista me za ki iya bayyanawa dangane da jin dadin aikin Lauya, ma’ana jin dadin da ke cikin aikin Lauya?

Eh, abin da nake so in bayyana a cikin aikin Lauya shi ne, na san hakkin Maza, Mata da hakkin yara, wanda ba shi da iyaka da na kwato masu ‘yancinsu a cikin shekarun da Allah ya ba ni a matsayina na Alkali. To yau, idan ka zauna ka yi la’akari a kan abin da za ka bari a Duniya, ba sai ka ba mutun kudi ba ko kuma wani abu a’a, yanda ka taba rayuwan wani shi ne kawai abin da kake da shi da za ka bari a Duniyan nan. Yau za ka zauna, idan ka shiga wani waje sai ka ga wani yana tsugunawa yana gaishe ka, domin ya ga babba, har ma ka ji kunya. Ya ce abinda kikai min na gode kuma ina ta yi miki addu’a kuma Allah ya yi miki albarka. Toh wani abin dadi ya wuce wannan, domin ba bu inda za ka je ba a girmamaka ba, za a nu na maka cewa wannan ya fa san abin da yake yi, ai ko ta fannin mijinka zai fa ji dadi har ma ya dunga tambayan ka shawara, kai da karfin ma da kuma burin mijin ka zai je ya shiga kowace talla da zai yi, ya san yana da Lauya da za ta nuna mishi hanyar da ya kamata ya yi da kuma abin da bai kamata ya yi ba, ko ba gaskiya ba, ko gida kake kai daya Lauya sai ka ga da kai ake ji, ana kawo maka kara, wannan ya faru wannan ya dauke min kudi wannan bai ba ni  kudina ba da dai sauransu. To ka gani, girmanka da ni’imanka daban yake da na kowa, kuma yana da dadi sosai kuma da riba da ba bu iyaka.

To kamar wanda ba zai iya bambanta aikin Lauya da aikin Alkalanci ba, shin me ya bambanta wadannan ayyukan biyu?

To shi aikin Lauya, idan kana aikin Lauya za ka je Chamber, ko ka na aiki da ma’aikatar Shari’a, to shi Lauya ba ya yanke hukunci, bambancin su kenan. Amma da Lauya da Alkali duk a makaranta daya suke karatu, za ku je makaranta ku yi digiri daya sannan ku je makarantar Lauyoyi. Amma wadansu ne za su je chamba, amma wadansu kuma za su tsaya a Lauya, to shi Lauya shi ne zai kawo magana a gaban Alkali. Alkali kuma na shi ya ji maganar da Lauya zai ce sai ya zauna ya tantance sai ya yanke hukunci, wannan shi ne bambancin su kenan kawai. Wasu da yawa daga cikin Mata suna da raunin zuciya kuma ga shi ke har kin taka matakin alkalanci wanda ake ganin ko Maza ma wani lokaci wajan yanke hukunci sai sun yi abin da ake cewa ta Maza, to ya ki ka ji da wannan aikin kasancewa ga ki Mace?

Eh, ai kasan duk abin da kai ka sa ma zuciyanka a kan ga inda ka ke so ka kai kuma dole wannan aikin kafin ka fara yin shi za ka je ka dauki alkawari tsakaninka da Allah, duk abin da ka ke yi kafin ka yanke hukunci, ko ka ki ko ka so, dole ka bi abin da duk aka ce domin ba kai ne ka yanke masu hukunci ba. Ko da ba ka san shi ba, ko ka san shi, dole ne ka cire wannan daga zuciyanka. Domin a matsayinka na Alkali ba zai yiwu ba ka sa raunin zuciya  wajen yanke hukunci, dole ne ka natsu ka yi abin da ya kamata. Na’am, wasu da yawa za su so su ji daga lokacin da ki ka fara sha’awan wanna aikin na Lauya?

Eh to, zan iya cewa tun lokacin da nake Jami’a, a lokacin na ga ya kamata a ce ni ma in karanta wannan aikin na Lauya, domin in taimaka ma Mata da suke cikin wani mawuyacin hali,  ya na mata nauyi wajen zuwa Kotu, sai su ga idan an kai ka kutu suna dauka kaman an bata maka suna ne, shi ya sa suke wahala, shi ya sa idan na je Kotu sai in yi kokarin jawo ra’ayin Mata da Maza domin kuwa Kotu ba wajan bata suna ba ne, wajen gyara ne. Idan ana gyara abubuwa za a samu zaman lafiya da kwanciyan hankali, kuma wanda ya taka maka za a fitar maka da hakkin ka, yanda kai ba za ka iya fitar da hakki a kan shi ba. Wannan shi ya sa na samu wannan burin, kuma na gode ma Allah Alhamdu lillah na taimaka sosai ta wannan fannin.

Zuwa yanzu masu karatu za su so su ji ko akwai kalubalen da ki ke fuskanta tun daga lokacin da kike karatun wannan Lauya har zuwa lokacin da ki ka fara aikin Lauyan da kuma Alkalanci, kafin mu zo kan wannan bangaran hukumar taki?

Eh, ai dole ne in kana aiki za ka ga abubuwa da yawa da ke taba maka kwakwalwa, daya daga ciki shine wanda har gobe damu na, in na tuna sai na zubar da hawaye, shine wanda aka kawo min yarinya ‘yan shekara hudu da aka yi mata fyade. Wallahi ranan gaskiya hankalina ya matukan tashi, kuma dattijo ya yi mata fyaden ba yaro ba. Hankali na ya tashi a kan yanda muke sake a Arewa da yara mata kananu, za ka ga ana tambayan ina wane sai a ce su na waje su na wasa, ba a san ina yake shiga ba, shi ya sa ake kama su ana masu fyade wanda ba a sani ba, sai su ce ma yaro kar ka fada a gida, idan ka fada zan kashe ka, yaro ba zai taba fadi ba. To tun daga lokacin hankali na yake tashi a kan fyade a Arewa. Shi wannan tsohon dan shekara nawa ne? shekaran shi kusan hamsin da shida.

To Barista, bari mu dawo bangaren cikin aikin hukumar ki, katamaimai wane  aiki ne hukumarki ta fi mayar da hankali a kai a Jihar Neja?

Abin da muka fi mayar da hankali a kai sosai, shine kare hakkin yara mata da kuma maza, domin muna da wannan tunanin na cewa ai dana ne, ni na haifa ko me ye na ga dama zan mi shi, ba haka ba ne tun yaro ya na ciki, Allah ya ba yaron nan hakki, wato uwar ba ta isa ta ji tana shaye-shaye ba, yaron ya fito bai da hankali. Ka ga na farko ta danne mai hakki idan ta je tana shaye-shaye, idan ba ta je ta yi alluran rigakafi domin ya kare ta kar ta samu maleriya ba, sai ka ga yaro ya fito da wata matsala ta danne ma shi hakki. To a wannan wajen muna kula da wannan har yaro ya kai shekara goma shatakwas, duk inda aka samu wani rauni kamar wanda suke luwadi, wanda suke fyade, wanda suke tallace-tallace,  da barace-barace,  duk wannan ba mu san shi ba, doka ba ta yarda ba domin wannan duk ana takewa yaro hakkI ne. Domin idan yana da bakin magana zai ce  bai so, Makaranta yake so ya yi, ko shi yana so ya zauna a gida ya yi wasa tare da ‘yan’uwan shi.

To dangane da wannan aikin zuwa yanzu ko akwai wani kalubale da za mu iya cewa hukumar taku tana fuskanta ganin cewa kamar wadannan abubuwa akwai msu neman su karfafa su, kuma ga shi kun daura yaki da su, to wadanne irin kalubale  ne hukumar taki take fuskanta?

Eh to, babban kalubale da muke fuskanta a nan Jihar Neja shine rashin sanin cewa yanzu Gwamnanmu ya kafa wannan ofishin da zai fitar da hakkin yara, ka san a Arewa gaba daya ba wanda ya kafa irin wannan ofishin na kare hakkin yara sai shi Gwamna Abubakar Sani Bello, to mutane ba su san cewa wannan ofishin yana nan ba, kuma sai mutane su ga kamar cewa in suka zo ofis dinnan sai an biya kudi, to ka gani kai ne aka yi ma ‘yarka fyade kai ne kuma za a ce ka kawo kudi a je kotu ko Asibiti, a’a, mu a nan ofishin ba mu karban kudin kowa. Muna taimakawa wadanda suka aka zalunta ne, kuma mu tambbatar da hakkin yara, a hakan zan iya gaya maka cewa yanzu an samu wanda aka ba su daurin rai-da-rai a kotu a nan Jihar Neja, sun kai guda shida domin laifin fyade. Irin wannan abubuwan ba abin wasa ne ba. A haka kuma zan ce maka, yaran da muka mai da su zuwa makaranta ba su da iyaka a cikin Jihar Neja, sun koma zuwa makaranta. Abin da mu muke nema kenan domin mu karfafa ilimi a Arewa, a karfafa shi sannan kuma a daga shi. Idan mutane da yawa suka shigo ai ilimi zai tashi, Almajirai a haka ma yanzu mun dauki mataki muna yarjejeniya da malamai ba mu son barace-barace, muna so a gyara masu rayuwa, ai mutane ne ba dabbobi ba ne. Almajirai yaranmu ne, duk yaron wani ai yaron ka ne. To a haka muna so a daina barace-barace, yaran su zo su koyi karatu na boko da na islamiyya, su koma ga wajen muhallin da za su kwanta mai tsafta mai kuma kyau ba kamar dabbobi ba. Kananan abubuwan da muke yi kenan muna zuwa kowace Karamar Hukuma, muna zuwa anguwa-anguwa muna wayar da su a kan abin da ake ciki. Mun bude wani bangare domin a daina yin  shiru a fara Magana, idan abu ya faru da makocin ka, ka zo ka gaya mana ba sai mun ce kai ne kafada ba, a’a, ba mu fadan sunan mutum. Amma za mu dauki matakin da kai za ka ji dadi, kila ma dan uwanka ne yake yi amma ka san ba za ka iya gaya ma dan’uwanka ya daina wannan muguntan ba, in ka zo wajen mu mu kan taimaka a gyara wannan sai ka ga mutane hankalin su ya kwanta a kan irin wannan abin.

Barista a halin yanzu muna so mu tambaye ki, wadannan ayyukan da ki ke gabatarwa ayyuka ne da suke bukatan lokaci sosai, to ya yi ki ke tafiyar da batun iyali da kuma wannan aikin naki musamman wajen kula da maigida?

Ka gani akwai abin da in ka fara kuma ka kai wani shekaru a rayuwa, tun ina cikin makarantar koyon aikin Lauya na yi aure, lokacin nan na san cewa maganan gida dole ka ware lokacin Maigida. Sannan  aiki dole ka ware lokicin aiki ba a hadawa ko ba gaskiya ba, ma’ana ban kawo aiki na gida, aiki na na san da ba mu da sati ba mu da lahadi, ban kuma kashe wayata daga safe har zuwa dare domin ko sha biyun dare a kan kira ni cewa wata yarinya tana cikin wani hali. To Maigidana na taimaka min saboda shi ya gane abin da ake ciki, ba wai zan fita karfe shabiyun dare ba, dole in ba shi hakkin shi domin shi yana gida sai in girmama shi, amma ya riga ya yarda min duk lokacin da za a yi waya in amsa, to zan amsa waya sai in kira masu aiki na ofishina domin su je wajen, tun da safe har zuwa lokacin da za a tashi daga aiki ai ina ofis duk abin da za mu yi ai za mu yi. Daga bayan ofis kuma zan dawo gida, ina so na zauna da iyalaina da kuma Maigidana domin mu zauna mu taimaka ma juna.

Barista da yawa za su so su ji yanayin yadda kike tarbiyantar da yaranki, a matsayin ki ta mace mai ilimi?

Yarinyata, sunanta Fa’iza, yanzu tana ma makaranta tana karanta aikin Injiniya a nan Abuja. Yarinya ce mai kokari a gida in ma lokacin hutu ya zo tana daukan Kur’ani tana karantawa, kuma tana zuwa makarantar Islamiya tare da koyon littafanta kuma yarinya ce mai son yin sana’a kala-kala kullun tana yin wani sana’a ko su na yin wani abu, amma ba sana’ar da zai saka ta fita waje ta tsaya daga safe zuwa yamma a waje a’a. Da safe da ma in aka tashi dole sai an tsaftace gida a yi abinci,  lokacin ne za ta shiga yin nata sana’an da take da ko wani abin da za ta yi, in ta gaji sai a tsaya ayi kallon Talbijin idan aka gama kuma sai a wuce Islamiya. To wannan a matakin da ta girma kenan, lokacin da take tasowa fa domin da yawa mutane suna ta’allaka matsalolin tarbiyan da ake samu na yara ana bari ne tun daga tushe, to ya kamata ki zama abin koyi ga wanda za su karanta wannan tattaunawar muna so muji daga lokacin da ki ka   haifeta abubuwan da ki ka kula da su, har kuma Allah ya sa ya zo ta samu karin natsuwa don ba za a ce kawai daga ta tashi ne da kanta ta natsu ba dole akwai abubuwan da ki ka kula da su, za mu so ki bayyana wa masu karatu wannan? To ka gani kamar lokacin da take tasowa a matsayin ‘ya mace, da ta fara shiga cikin mutane kamar abokanai sai ta zo tana son in aka ba ta kaya takai dinki, ka san yara mata sai su je su dinka shi ya matse, a lokacin ban mata fada ba, sai na kira ta nace to ga abubuwan da ki ke yi, a hakan nan ita da kanta ta daina irin wannan dinkin. Ka gani yaro sai ka bi shi a hankali, ban da wannan kuma sai na zo da illan maza har ila yau, ka san ‘ya mace kamar zuma take wannan ya zo wannan ya zo, a lokacin ma sai na zaunar da ita na gaya mata ga fa illar harkan namiji. A nan Arewa ina rokon mata har ma da iyaye ma a zauna a bayyana ma yaron maganar saduwa da wani domin ya san abin da yake ciki ba wani ya gaya mi shi karya a waje ya dauka ba. Haka din ma makarantar Islamiya domin ka san yara idan suna girma za su kai wani lokuta da ba za su so zuwa makaranta ba dole sai ka tilasta masu zuwa Islamiya domin kan haifar da ba ka haifi halin shi ba, amma idan addinin nan ya shiga jikin su, duk lalatan da za su yi  da yardan Allah zai zo da sauki insha Allahu.

Barista dazu kin yi maganar abin da ya shafi zamantakewa na gidanki, to yanzu zamu so ki kalli zamantakewa ta mata da mazajansu a Arewa, me za ki ce a halin da ake ciki? A halin da ake ciki a Arewa, ni ina rokonmu, mu rika la’akari da abin da Manzo ( S.A.W.) ya yi ga matan shi, domin maza su yi ma matan su, gida ba na mata ba ne su kadai, idan ka auri mace saboda ka na son ta ne, wacce za ka zauna da ita har ranar da Allah zai dau ranka. Amma ba ka auri mace ba saboda kai ka fita waje ka barta ita kadai a gida, ta yi ta hidima da yara ba abin da ya dame ka, a’a, ba a hana ba idan kana so ka kara aure kuma Allah ya yarda maka ka yi har guda hudu, amma idan ana gida kai ma ka ba ta lokacinta da kuma hakkinta a gida, ku hada hannu ku san abin da ke faruwa da yaranku, me suke yi, ina suka je, ina ne ba su je ba, amma idan ka ce ka bar mata ita daya,kila tana aiki ita ma ta dawo ta gaji, idan kuma ba ta aiki kila ba ta da wannan natsuwan ballantana ta ce bari ta duba kila yaro yana nan yana shaye-shaye, har yaro ya yi nisa ba ka sani ba ko yaro ya je yana nan yana zuwa sata kai ba ka ma sani ba, ko kuma rashin kula haka, to ka gani dole in roki iyaye maza da mata a Arewa da ake aure a dunga nu na ma juna soyayya sosai don a kullum ita mace tana neman mijinta ya dunga nu na mata mene ne za ki yi domin ta kara faranta mi shi rai, domin ba zai yiwu ba kai tana faranta maka rai kai kuma kana bata mata rai, dole za a samu mishkila. Kuma ba zai yiwu ba a ce za ta hada kanta da kai, domin kai ne mai gida dole ta girmama ka a matsayin ka na Maigida, amma dole ka taimaka mata ka hada hannu da ita, ka nu na mata soyayya ka zaunar da ita ka ji mene ne matsalolin da take fuskanta a gida, ta ya ya za mu tunkare su, a lokuta kuma ka dunga gaya mata tana da kyau kuma kana son ta, lokacin za ka ga mace ta samu buri a zuciyanta na kar ta bata maka rai, amma kai ka tashi kai kadai ka tafi aiki ka dawo da dare ka kwanta kawai  ba wani magana na me ake so a gida, haba ai ba kyau haka.

Barista ga shi mun dauko gangara amma za mu so ki yi ma masu karatu magana ta karshe, wacce watakila ba mu tambaye ki ba.

Wanda suke zuwa neman ilimi, abin da kawai zan gaya masu shine, kar kowa ya yarda wani ya rudad da shi a kan kar ya je ya nemi ilimi cikakken ilimi ko min shekarun ka ilimi ba zai taba wuce wa a banza ba kuma ilimi shine mutum a duniyan da muke ciki a yanzu domin shine zai taimake ka. Idan kana da ilimi  hatta Kur’aninka za ka iya ka kara wa kanka ilimi idan ka tashi karanta shi, idan ma sana’a kake yi zai taimake ka yanda za ka tarbiyantar da yaranka, idan ka na da ilimi yafi karfi a kan wanda bai da ilimi sai ka ga harshen da kowa ya ke yi daban ne. idan kana makaranta don Allah mata ina rokon ku, kar ku yadda wanda suka wuce shekara goma sha takwas wani da namiji ya rudad da ku a kan aure, domin a bar makaranta a ce mu yi aure in ki na gidana zan saka ki makaranta a’a, a shiga makarantan tukunna don Allah, ana aure aka samu ciki maganat makaranta ta shiga ruwa, ma’ana ta kare. Maza su kuma don Allah daga na  farkon shan wi-wi din nan shike nan ba ranan bari, kuma domin abokanai za su ce kai da Allah ka ji yaron Mama, gwanda ka tsaya a matsayin yaron Mama da ka tsaya a matsayin mahaukaci a kan titi, shawara na kenan.

Zuma times

2 thoughts on “YADDA MUKE GWAGWARMAYAR KARE HAKKIN MATA DA YARA A NEJA — BARISTA MARYAM KOLO

Leave a Reply

Your email address will not be published.