Ba abin da zai hana ni zuwa Kano — Kwankwaso

News
Senator Rabiu Musa KwankwasoHakkin mallakar hotoFACEBOOK/KWANKWASIYYA REPORTERS

Wani na hannun daman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Comrade Aminu Abdussalam ya ce babu gudu babu ja da baya game da ziyarar da tsohon gwamnan Kanon ya shirya kai wa kano a karshen wannan watan.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya “Rubuto wa Sanata Kwankwaso cewa suna ba shi shawara cewa akwai wasu mutane da ka ce sun yi shiri za su je su tayar da tarzoma a wurin taron da zai haifar da wani abu mara dadi”.

Ya kuma kara da cewa: “Saboda haka ‘yan sanda suna ba shi shawara da ya janye zuwansa Kano.”

Ya kuma ce ‘yan sandan sun rubuta watohon gwamnan takarda inda suke ba shi shawarar dage wannan ziyara da ya shirya kaiwa Kano.

Amma da alama Sanata Kwankwason bai karbi wannan shawarar ta ‘yan sanda hannu bibiyu ba:

“A matsayinsa na dan kasa kuma daya daga cikin jagorori na siyasar Najeriya, ya rubuta musa cewa ya ga takardarsu, kuma a iya fahimtarsa, aikin jami’an tsaro ne su tabbatar da tsaro, ba ma nasa ba, amma na al’ummar kasa duka,” inji Comrade Aminu Abdussalam.

  • Zuwan Kwankwaso Kano na da hadari —’Yan sanda
  • An raba gari tsakanin Ganduje da mataimakinsa ne?

Ya kara da cewa kamata yayi ‘yan sanda su dauki mataki akan wadanda suke kitsa wannan tashin hankalin.

Dangane da ko sun dauki shawarar ta ‘yan sanda na cewa su dage wannan taro a Kano, ya ce: “Matsayin da muka dauka shi ne, a bisa doka da tsarin mulkin Najeriya, wajibi ne ga jami’an tsaro da kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya tabbatar da tsaro ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ma duk wani mutumin Kano da tabatar da cewa sun yi harkokinsu ba tare da tsangwama ba”.

Takardama

Comrade Aminu Abdussalam ya bayyana cewa “kwamishinan ‘yan sanda ya hana jami’ansa karbar wannan takardar da muka kai musu.”

Ya musanta cewa ‘yan sanda sun ba su shawarar janye nasu taron ne saboda bangaren gwamna Ganduje sun riga su mika bukatar gudanar da nasu taron gabanin mika bukatar da bangaren Sanata Kwankwaso ya yi.

“Ba haka suka gaya mana ba. Kuma a rubuce suka ba mu takarda. Cewa suka yi wasu sun shirya za suyi ta’adda a wannan lokaci, ba zasu so Sanata Kwankwaso ya shigo a yi masa ta’adda ba.”

Ya kuma ce ‘yan sandan “Suna ba shi shawara kada ya zo, har sai yanayi ya inganta. Har sai yanayi ya inganta. Ba inda suka yi mana zancen wani ya ce zai yi taro a ranar da za muyi taro, ko a gurin da za muyi taro.”

Ya bayyana makasudin wannan ziyara: “Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai zo jiharsa ta haihuwa… Zai kuma je gidansa a Gandun Albasa, ya gaisa da masoya da magoya bayansa da sauran al’ummar jihar Kano manya da kanana”.

Comrade Aminu ya kuma musanta cewa bangaren Kwankwasiyya sun shirywa wani taro ne a Kano.

“Mu ba mu fasa ko wane shiri ba, kuma muna kara jaddadawa hukumar ‘yan sanda da jami’an tsaro na Kano cewa wajibinsu ne su bada tsaro ga Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da al’ummar da zasu zo tarbarsa.”

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *