Sakin fim din Padmavati ya janyo zanga-zanga a India

Entertainment
Ana zanga-zanga a India saboda sakin fim din Padmavati na BollywoodHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionAna zanga-zanga a India saboda sakin fim din Padmavati na Bollywood

Masu zanga-zanga a jihar Gujarat ta kasar India, sun toshe hanyoyi tare da dakatar da zirga zirgar motocin bas, bayan kotun kolin kasar ta bayar da umarnin sakin fim din nan na Bollywood da ke janyo ce ce-ku ce wato Padmavati a ranar Alhamis.

Masu tsattsauran ra’ayi na addinin Hindu, sun kona motocin bas da kuma kwasar ganima a wata sinima da ke yammacin jihar ta Gujarat.

Ce ce kucen ya samo asali ne bayan da wasu kungiyoyi na addinin Hindu wato ‘yan bangaren da sarauniyar ta fito, suka ce, a lokacin da aka fito da tallan fim din, an nuna wani wuri da aka bata sunan sarauniyar, inda aka nuna ta da wani sarki musulmi, Alaudin Kilji, suna soyayya.

Wannan dalili ya sa suka ce, an ci mutuncin sarauniyar, kuma hakan ya sosa musu rai, don haka sam ba za su amince da fim ba, ballantana a sake shi har duniya ta gani.

Kotu ta amince a saki fim din Padmavati

An ci zarafin jarumar fim din Dangal Zaira Wasim a cikin Jirgi

An dai ta kai ruwa rana game da haramcin fim da wadan da suka fito daga bangaren sarauniyar suka ce, domin har kotu aka je, daga karshe kuma kotun kolin kasar ta amince da a saki fim din, bayan ta umarci wanda ya shirya fim din, Sanjay Leela Bhansali, da ya cire duk wasu wuraren da basu kamata ba a cikin fim din.

Fim din na Padmavati, labarin fim din wata kyakkyawar sarauniya ce daga bangaren mabiya addinin Hindu wadda aka taba yi a karni na 14, tare da wani sarki musulmi.

Wannan dai ba shi ne fim na farko da aka taba yi wa zanga-zanga a India ba.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.