TAKAITACCEN TARIHIN JANAR IBRAHIM BADAMASI BABANGIDA.

Literature

Fatan Alheri gareka Dattijon Kirki mai kishi da tausayin

Al’umma An haifeshi ranar Lahadi 17, ga watan August 1941 a Garin Minna. Sunan kakansa Mallam Audu Najoji wanda shi Malami ne mai wa’azi a Garin Wushishi, wanda a nan ya zauna bayan yin hujirarsa daga kano, kakarsama tana cikin wanda sukayi hijira zuwa garin Wushishi, wacce ita kuma iyayenta daga Sokoto, suka taso. An haifi Mahaifin Babangida Muhammadu Badamasi a Garin Wushishi, amma ya tashi da iyalansa ya koma Garin Minna a 1936, Mallam Badamasi, ya rasu a Garin Kontagora a 1955, Mahaifiyarsa Aisha ta rasu 1956, cikin yaran Badamasi, guda biyu kawai suka rayu. A cikin 1950 ansashi a makarantar Lardi ta Minna, ya wuce babbar firamari ta Minna a 1954, ya kammala 1956, a cikin 1957, ya shiga makarantar Sakandiri a Bida, kammala karatun Sakandiri a shekarar 1962. Ranar 10 ga watan December, ya shiga aikin soja. Ya shiga kwalejin ya ye manyan hafsoshi ta kaduna NMTC, kafin ta zama NDA, sune kwas na 6. Bayan kammala kwas na shekara daya, Babangida ya wuce kasar Indiya ya halarci Dehradun ya kammala a 1963, ya kuma zama cikakken soja a cikin watan September 1963, ya kuma daura anini daya. A cikin shekarar 1966 ya sake komawa wani kwas a Ingila, bayan kamnala kwas din a 1966, ya daura anini biyu. Bayan shekara daya ya sake komawa wannan makarantar yin wani kwas.

Ya dawo Najeriya daga kasar Ingila a 1967, yakin Basasa, ya barke, antura Babangida, bakin daga inda aka fara turashi shi Nsukka, ankai shi karkashin Birget din Inuwa Wushishi, bayan kwashe shekara daya cir a bakin daga ankaramai Girma zuwa Kyaftin kuma aka bashi kwamandan infantiri Bataliya ta 44. Kyaftin Babangida ya samu rauni a cikin watan April 1969, a Uzuakoli, bayan ya samu sauki ya sake dawowa fagen fama, an ci gaba da fafatawa da shi har aka gama yaki. Ya daura mukamin Manjo cikin watan April 1970, ya kuma sake komawa wani kwas a Warminister, a Ingila na kamfani Kwamanda. A 1970, ya zama mai bada horo a kwalejin NDA kaduna, a 1974, ya zama Laftanal Kanal kafin nan sai da ya sake zuwa wani kwas a 1972, a Ingila a fort knox. Bayan samun chanjin Gwamnati a ranar 29 ga watan july 1975, Babangida, ya zama danmajalisar koli ta mulkin soja, kuma a wannan shekaranne ya zama mai horarwa a sashin kula da tankokin yaki amma a lokacin bai rike da mukamin siyasa. Babangiya, ya yi fucene a rawar da ya taka wurin murkushe yunkurin juyin mulkin da Dimka, ya yi na ranar 13, ga watan February 1976. Yanda ya tunkari Dimka, a harabar gidan rediyo na Ikoyi.

@faces

3 thoughts on “TAKAITACCEN TARIHIN JANAR IBRAHIM BADAMASI BABANGIDA.

  1. Im still learning from you, while Im making my way to the top as well. I absolutely enjoy reading all that is posted on your site.Keep the stories coming. I liked it!

  2. This is some useful stuff. It took me a while to unearth this web page but it was worth the time. I noticed this website was hidden in google and not the first spot. This site has a lot of good quality stuff and it does not deserve to be burried in the searches like that. By the way I am going to add this weblog to my favorites.

Leave a Reply

Your email address will not be published.