Kamfanin Apple ya nemi afuwar abokan huldarsa

iPhoneHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionWayar salula samfurin iPhone na da farin jini musamman tsakanin matasa

Kamfanin Apple da ya yi fice wajen samar da wayoyin zamani na komai da ruwanka, ya nemi afuwar abokan huldarsa kan gwangen da ya yi kan wayar iPhone rage saurin wasu tsofaffin wayoyin da gangan.

Masu hulda da kamfanin sun dade suna zargin kamfanin Apple na ragewa tsofaffin wayoyin hannu sauri, musamman idan ya na gab da fitar da sabuwar wayar iPhone, domin a tilastawa musu amfanin wayar sayen sabuwar fitowa.

Kamfanin ya ce ya na shirin kara inganta wayoyin salular, da sanya matakan kare ta daga lalacewa baki daya.

Apple ya yi alkawarin zai rage farashin batirin wayar sanfurin iPhone 6 da wasu sabbin wayoyin idan ya fitar da su.

Haka kuma ya ce zai samar da wata Saftiwaya da za ta bai wa maso amfani da wayar damar samun bayanan sirri da suka shafi ingancin wayar.

A tsakiyar watan nan ne, Kamfanin Apple ya tabbatar wa masu wayoyin iPhone cewa yana rage saurin wasu tsofaffin wayoyin na iPhone da gangan.

Masu hulda da kamfanin sun dade suna tuhumar kamfanin Apple din da rage wa tsofaffin wayoyin hannu na iPhone sauri domin a tilasta musu sayen sababbin wayoyin da suka fito.

Kamfanin ya fito fili ya bayyana cewa lallai yana rage wa wasu wayoyin sauri domin karfin batirin wayoyin na raguwa bayan wasu shekaru.

Apple ya ce yana yin haka ne domin ya “tsawaita ran” na’urorin da yake kerawa.

Lamarin ya fara bayyana ne a lokacin da wani mai amfani da wayar Iphone ya wallafa rahoton wani gwaji da ya yi a shafin intanet na Reddit, a inda ya nuna cewa wayarsa samfurin iPhone 6S ta rage sauri matuka amma ta fara saurin sosai bayan da ya sauya tsohon batirin da sabo.

“Na yi amfani da wayar dan uwana samfurin iPhone 6 Plus, kuma na lura wayar tasa ta fi tawa sauri.

“A lokacin ne na tabbatar cewa akwai lauje cikin nadi,” inji mawallafin rahoton mai suna TeckFire.

Daga nan ne shafin fasahar yanar gizo, Geekbench ya binciki samfurin wayoyin iPhone masu amfani da manhajar iOS daban-daban, inda ya gano cewa lallai kuwa ana rage musu sauri da gangan.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *