Cutar farankamar biri ta bazu a jihohi 23 a Nigeria

Karanbon Biri ta bazu a jihohi 23 a NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKuraje da zazzabi mai tsanani da radadi na daga cikin alamomin cutar

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa cutar farankamar biri, yanzu ta bazu a jihohi 23 daga cikin 36 na kasar.

Sama da mutane 60 aka tabbatar da sun kamu da cutar wacce ta fara bulla a watan Satumba, yayin da kuma aka tabbatar da mutuwar mutun daya.

Ana kamuwa da cutar wacce yanzu ta zama annoba daga birai da beraye da kuma dabbobin daji.

Sannan cutar na yaduwa tsakanin mutane.

  • An killace mutum 60 a Kano saboda kyandar biri
  • Annobar kyandar biri ta barke a jihar Bayelsa da ke Nigeria
  • Nigeria: Sabon rikici ya barke a jam’iyyar PDP

Kuraje da zazzabi mai tsanani da radadi na daga cikin alamomin cutar. Kuma har yanzu ba a samu maganin warkar da cutar ba

Tun bullar cutar a jihar Bayelsa, hukumomin lafiya a Najeriya suke ta yin gargadi ga jama’a da su guji cin naman biri da sauran namun daji kamar kurege da sauransu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *