An gano kwarangwal mai ‘shekara miliyan uku’ a Afirka Ta Kudu

Reports
Little Foot's skeleton
Image captionMasana kimiyya sun yi amannar cewa hakan na nufin asalin dan adam dai ya watsu a sassa daban-daban na Afirka tsawon lokaci

An kaddamar da wani kwarangwal wanda aka yi amannar ya kai shekara miliyan uku a Afirka Ta Kudu.

Wata tawaga ta shafe shekara 20 tana aikin tono shi da goge shi da kuma hada sassansa waje daya.

An tafka muhawar dai kan yawan shekarun kwarangwal din, amma masana kimiyya na Afirka Ta Kudu sun ce zai kai shekara miliyan 3.67.

Hakan na nufin wannan kwarangwal da aka yi wa lakabi da Little Foot dai ya shafe shekara 500,000 kafin kwarangwal din Lucy, wanda a da aka yi amannar shi ne mafi dadewa a duniya, wanda aka gano a Habasha.

Da Little Foot da Lucy dai dukkansu sun fito ne daga jinsin Australopithecus, amma suna da bambancin asali.

Masana kimiyya sun yi amannar cewa hakan na nufin asalin dan adam dai ya watsu a sassa daban-daban na Afirka.

Farfesa Ron Clarke ne yagano Little Foot a wani kogo da ke arewa maso yammacin birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu.

Ana tsammanin kwarangwal din wata matashiya ne da ta fada can cikin kogon.

“Kwarangwal din zai iya kasancewa karami, amma dai yana da muhimmanci. Saboda ya taimaka mana wajen gano asalinmu,” in ji Farfesa Clarke.

Stephen Motsumi and Nkwane MolefeHakkin mallakar hotoPAUL MYBURGH
Image captionTawagar ta shafe shekara 20 tana aikin tono kwarangwal din da goge shi da kuma hada sassansa waje daya

Ya kara da cewa: “An sha wahala kwarai wajen ciro kasusuwan kwarangwal din daga kogon, saboda kasusuwan sun yi laushi kwarai, kuma sun nutse cikin kogon.”

“Sai da muka yi amfani da wasu kananan kayan aiki kamar allurai don ciro su. Shi ya sa aikin ya dauki lokaci mai tsawo,” in ji Farfesa Clarke.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *