PDP ba za ta bai wa Atiku takara ba sai…

Politics

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta ce ba za ta bai wa tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar takarar shugabancin kasar a inuwarta ba, sai ya bi dukkan matakan da aka shimfida.

Shugaban riko na jam’iyyar ta PDP Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ne ya fadi haka a hirarsa da BBC.

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasar ne da kansa ya yanke shawarar komawa PDP ba jam’iyyar ce ta yi zawarcinsa ba.

Ya kara da cewa suna matukar murna da komawar tasa cikin jam’iyyarsu.

  • Me ya sa APC ta kasa zama dunƙulalliyar jam’iyya?
  • Mutum miliyan uku sun rasa aiki a lokacin Buhari — Atiku

A ranar Lahadi ne Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP a shafinsa na Facebook.

Ya zargi jam’iyyar APC da kin cika alkawuran da ta yi wa ‘yan kasar, yana mai cewa: “Gwamnatin APC ta yi alkawarin samar wa mutum miliyan uku aiki a ko wacce shekara amma mutum miliyan ukun ne suka rasa aikinsu a lokacinta”.

Sai dai bai fito fili ya bayyana anniyarsa ta sake neman shugabancin kasar a babban zaben kasar na shekarar 2019 ba.

Ya ce ya koma jam’iyyar ne saboda matsalolin da suka sa ya fice daga PDP a shekarar 2014 “an warware su yanzu.”

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari gwamnatin Shugaba Buharin ba ta mayar da martani ba.

Sanata Makarfi ya ce ba PDP ce ta yi zawarcin Atiku baHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA baya Atiku ya ce ba zai sake komawa PDP ba

Amma a baya sun sha yin watsi da wasu zarge-zargen da Atikun ya sha yi kan jam’iyyar APC da ma mulkin Shugaba Buhari.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *