Karin kudin wuta: Akwai almundahana a ciki – kungiya

News

 

Wata kungiya mai suna Electricity Consumers Protection Forum, watau, zauren masu kare hakkin masu amfani da wutar lantarki ta bayyana cewa akwai almundagana a cikin karin kudin wuta da kuma saida masana’antar da wuta.

fashola i

Ministan wutar lantarki, Babatunde Raji Fashola

Kungiyar ta bayyana wannan ne a Legas aranar 8 ga watan Fabrairu inda ta bayyana cewa cikin wadanda aka saida ma masana’antar, Kamfani 3 ne kawai suka kammala biyan kudin.

Kungiyar ta bayyana cewa wuta bata samuwa sosai amma duk da haka gwamnati na son ta kara kudin wuta wanda hakan kwata kwata bai kamata ba.

Kungiyar tayi Allah wadai da wannan yunkuri sannan kuma ta bukaci gwamnati tayi ma masana’antar garan bawul. Idan za’a iya tunawa, anyi zanga zangar nuna kin amincewa da karin wutar lantarki a ranar Litinin 8 ga watan Fabrairu inda kungiyoyin kwadago dana yan kasuwa suka jagoranci zanga zangar.

NAIJ.COM