Nigeria ta auna arziki a taron OPEC

News
OPECHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionOPEC ta yaba wa kokarin Najeriya wajen farfado da harkokinta na tattalin arziki a shekara ta 2017

Taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da ma wadanda ba ‘yan kungiyar ba irinsu Rasha ya amince ya kara wa Najeriya wa’adin shekara guda kafin ta farfado har ta fara rage yawan man da take hakowa.

Kungiyar OPEC da sauran kasashe masu arzikin man fetur sun gudanar da taron ne ranar Alhamis a Vienna babban birnin kasar Austria don bitar manufar kayyade yawan man fetur din da suke hakowa.

Manufar tun da farko ta yi wa kasashen Najeriya da Libya da Iran togaciya, saboda matsaloli da rikice-rikicen da suke fama da su a cikin gida.

An yi ta bayyana fargabar cewa taron na Vienna zai tilasta wa kasashen da aka yi wa togaciyar, su ma a wannan karo su rage yawan man da suke hakowa, bayan an amince sauran kasashen su ci gaba da rage nasu man.

Babban Sakataren OPEC, Alhaji Muhammad Sanusi Barkindo ya fada wa BBC cewa taron wanda kasashe guda 30 suka halarta a ciki da wajen OPEC ya yi bitar nasarorin da aka samu tun watan Janairu zuwa yanzu kuma ya amince a ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsawon shekara daya.

Ya ce: “Kamar yadda dai muka zartar a watan Disamban bara, mu cikin OPEC za mu rage ganga miliyan daya da 200,000, su kuma kasashen da ba sa cikin OPEC za su rage ganga 600,000, ya kama ganga miliyan daya da 800,000 a kullum.”

Barkindo ya ce taron ya nuna farin ciki da kokarin da gwamnatin Najeriya take yi musammam a wannan shekara don tabbatar da ganin ta koma tana hako adadin man fetur din da take muradi.

“Amma har yanzu ya kamata a ba su lokaci don ci gaba da samun nasarorin da suke samu, har tattalin arzikin kasar ya dawo kamar yadda yake a baya, in ji shi.

Matakin dai na da gagarumin tasiri ga tattalin arzikin Najeriya musammam a wannan lokaci da wasu masana ke cewa kasar na fuskantar kalubalen aiwatar da kasafin kudinta na 2017 saboda karancin kudin shiga da take samu.

Wani masanin tattalin arziki a Jami’ar Bayero Kano, Dr Ahmad Muhammad Tsauni ya ce bisa la’akari da kasafin kudin Najeriya na 2018… za ka ga cewa kudaden da aka sa ran za a samu, wadanda za su taimaka a iya aiwatar da kasafin kudin, ba za su iya samuwa ba.

A cewarsa: “Idan ka dubi abin da ke gudana a wannan shekara da muke ciki, yadda aiwatar da kasafin kudin ma ya gaza kashi 20 cikin 100, ba don wani abu ba sai don rashin kudi.”

Kullum maganar ita ce kudin da ake sa ran za a samu, ba a samu ba. Wannan shekarar kenan ballanatana shekarar da aka lafta wannan kudi makudai, da ake sa ran aiwatar da kasafin kudi na gaba, in ji shi Dr. Tsauni.

Ya bayyana damuwa kan yadda Najeriya ta dogara kacokam kan man fetur a matsayin hanyar samun kudadenta na shiga.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *