Tirkashi! Gwamnati ta ce a tattaro mata kudaden da ba’a yi wa asusun bankin su BVN ba

News

An sa dokar kowa sai ya yi wa asusun bankin sa BVN tun a shekarar 2014 – Har yanzu akwai asusan da ba’a yi musu ba, wanda ya kawo biliyon kudi a ajiye kawai turus – Gwamnati ta ce a tattaro mata su in ba masu shi Kotin koli ta kasa ta baiwa gwamnati dama da a tattara mata kudaden asusan bankunan da ba’a yi musu BVN ba. Shugaban lauyoyin kasa, Abubakar Malami, ne ya shigar da wannan neman izinin da yawun gwamnati. Ana kyautata zaton cewa wadannan kudaden a kalla sun kai biliyoyin Nairori, daloli, da fam-fam — suna zaune a bankuna turus kawai ba’a amfani da su.

Naij.com

Leave a Reply

Your email address will not be published.