Nigeria: Za a kwace kudaden wadanda ba su da lambar BVN

News
BVNHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionAn kaddamar da dokar tilasta amfani da BVN din ne domin a dakile almundahana a bankunan kasar

An bai wa gwamnatin Najeriya ikon karbe kudaden da aka ajiye a asusun bankunan kasar wadanda ba su da lambar bayanai na BVN ba.

Akwai kimanin asusun ajiyar kudi a banki miliyan 46 wadanda ba su da lambar bayanai na BVN na wadanda suka mallake asusun a Najeriya.

A karshen mako ne gwamnatin Najeriyar ta samu kotu ta ba ta damar rufe irin wadannan asusun marasa lambar BVN a wani mataki na yaki da cin hanci da rashawa.

Duk da cewa gwamnatin ba ta kiyasta adadin kudaden ba, an yi imanin cewa biliyoyin naira da kuma miliyoyin daloli ne kudaden da suka makale a cikin asusun mutane a bankuna ba tare da lambar bayanai ta BVN ba.

A halin yanzu dukkan wadannan kudadensu sun makale har sai masu kudaden sun gabatar da lambarsu ta BVN kafin su sami kudaden.

An bai wa bankunan umarnin su wallafa bayanan masu wadannan asusun ajiyar a jaridu domin masu ruwa da tsaki a lamarin su san halin da ake ciki.

Babban bankin Najeriya ne ya wajabta amfani da lambar BVN din a domin ta tattar bayanan masu ajiye kudi a bankuna da kuma dakile almundahana daga bankunana kasar.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *