Kun san hoton tukin mata da ya fusatar da ‘yan Saudiyya?

Reports
Faisal BaDughaish‏ and wife driving in a carparkHakkin mallakar hoto@BADUGHAISH / TWITTER
Image captionFaisal BaDughaish‏ da matarsa a wani wajen ajiye mota

Kwana uku bayan Sarki Salman ya ayyana dokar da ta bai wa matan Saudiyya damar tuki, wani hoton dauki-kanka-da-kanka (selfie) na wani mutumin da yake koya wa matarsa tuki ya janyo muhawara mai raba kawuna a shafin sa da zumunta na Twitter.

Faisal BaDughaish, wani manazarci ne a wani kamfanin iskar gas da mai daga Dhahran a gabashin Saudiyya wanda ya wallafa wani hoton kanshi da matarsa a wani wurin ajiye motoci mai zaman kansa.

Sakon da ya wallafa ya ce:”Na fara koya wa matata tuka mota, a daya daga cikin wuraren fakin mai zaman kansa a wani yanayi na aminci da na bin doka domin shirya wa lokacin da dokar za ta fara aiki.”

Jira cikin hakuri

Amman martanin da aka mayar wa hoton -wanda aka yayata sau dubban lokuta a shafin Twitter- ya nuna yadda soke dokar da ta hana mata tuki yake cike da ce-ce-ku-ce. Wasu sun ce sun ki amince da yadda Mista BaDughaish ya wallafa hoton da ya nuna fuskar matarshi.

“Ba ka jin kunyan ko kuma kareta yayin da kake wallafa hoton?” in ji sakon Bderr1991 wani mai amfani da shafin na Twitter .Sakon ya kara da cewa:”Ka ji kunya.”

Amman mata sun ba da amsa mai kyau ga sakon na Twiter, suna masu cewa su ma suna jiran koyon tuki daga mazaje cikin ‘yan uwansu. Wata mata mai suna Amal Nadhreen ta ce: “Gobe, da na Azzam zai koya min tuki.”

Wasu mazajen, kaman Faisal Alshehri, sun wallafa sakon Tiwtter cewa matakin da mista BaDughaish ya dauka na koya wa matarsa mota ya ba su kwarin guiwar koya wa matansu.

“Dukkanmu za mu bi sawun ka,” in ji shi.

  • Saudiya: An kashe masu gadin fadar Masarautar a wani harin bindiga
  • Abin da har yanzu mata ba su da izinin yi a Saudiyya?

Sai dai kuma, wasu mata sun ce dokar da masarautar ta fitar ta haifar da muhawara tsakanin ‘yan uwansu. Wata mai amfani da shafin Twitter mai suna Julnar ta wallafa sako mai cewa: “Zan sa da na ya koya min, duk da cewa miji na ya ce a’a- amman ni ba zan yarda ba.”

Da yake magana da Sashen Larabci na BBC, mista BaDughaish ya ce shi da matarsa sun dade suna jira cikin hakuri domin ganin ranar da za a sauya dokar ta Saudiyya kuma yana fatan cewa matakin da ya dauka zai karafafa wa sauran mazajen guiwa domin su koya wa ‘yan uwansu mata tuki.

Ya kara da cewar ya so karfafa wa mata guiwa domin su koyi tuki bisa ka’ida, domin a yanzu haka doka ba ta yarda mata su koyi tuki a kan manyan hanyoyin Saudiyya ba. Ya ki yarda da kokarin da aka yi na yin hira da matarsa kuma ya ce shi ba ya son ya ba da bayanai game da ita.

BaDughaish ya ce wasu daga cikin sakonnin da aka tura mishi suna cike da barazana, lamarin da ya sa shi ya kai karar su ga ma’aikatar Saudiyya da ke sa ido kan laifukan Intanet.

Wakilin Saudiyya na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ne ya fitar da shelar masarautar saudiyya mai cike da tarihi da ta bai wa mata damar tuki a cikin zauren MDD.

Mata a kasar za su iya tuki ne daga watan Yunin shekarar 2018.

Masarautar da ke yankin tekun Fasha ita kadai ce kasar da ta hana mata tuki a duniya- maza ne kawai suke da damar samun lasisin tuki, kuma za a iya kama ko kuma a ci taran mata masu tuki a bainar jama’a.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *