Kamfanin NNPC ya yi wa ministan man fetur raddi

Reports
Kanti BaruHakkin mallakar hotoALIYU ABUBAKAR FACEBOK
Image captionNNPC ya kuma ce dukkan kudaden da aka samu ta hanyar aiwatar da kwangilolin za a zuba su ne a lalitar gwamnati ba na kamfanin ba

Shugaban kamfanin mai na NNPC, Maikanti Baru, ya musanta zargin aikata ba dai-dai ba wajen bayar da ayyukan kwangila da ministan mai na Najeriya, Dr Emmanuel Ibe Kachikwu ya yi masa.

A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun kakakin NNPC, Ndu Ughamadu, ta ce zargin cewa shugaban kamfanin ya bayar da kwangilar da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 15 ba gaskiya ba ne.

Haka kuma kamfanin ya bi dukkan matakan da aka shimfida da kuma ka’idojin da suka dace wajen bayar da kwangilolin.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba a kayyade kudaden kwangilolin ba, saboda suna matakin yarjeniyoyi ne, kuma a karkashin doka kamfanin ba ya bukatar tattaunawa ko sake duba kwangiloli daga wajen ministan.

Sai dai manyan kwangiloli na bukatar amincewar kwamitin tantance kwangolili na kamfanin da kuma shugaban kasa a matsayinsa na babban ministan mai ko kuma majalisar ministoci ta kasar.

NNPC ya kuma ce dukkan kudaden da aka samu ta hanyar aiwatar da kwangilolin za a zuba su ne a lalitar gwamnati ba na kamfanin ba.

  • Nigeria: Takaddama ta kaure tsakanin karamin ministan mai da NNPC
  • Nigeria: Aikin hako mai ya yi nisa a Sokoto — NNPC
  • An kori manyan jami’an NNPC kan sakaci

Sanarwar ta kuma ce shugaban NNPC ya dinga tuntubar Dr Kachikwu a ayuykan kwangilar da aka bayar kuma ya yi amfani da shawarwarin da ya ba shi kan haka batun cewa ba ya ma tuntubarsa ba ta taso ba.

A karshen watan Agustan da ya gabata ne dai karamin ministan man ya rubuta wata wasika ga shugaba Muhammadu Buhari yana mai zargin shugaban kamfanin na NNPC da rashin bin ka’idoji wajen bayar da manyan kwangolili, da kuma rashin yi masa biyayya.

Wasikar da aka kwarmata ta janyo cece-ku-ce daga wasu masu ruwa da tsaki a fannin mai na kasar ciki har da kungiyar dillalan mai masu zaman kansu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *