INEC ta sake dakatar da yi wa Dino Melaye kiranye

News
Dino MelayeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionHukumar INEC ta ce a shirye take ta fara yi wa Sanata Dino Melaye kiranye da zaran kotun daukaka kara ta yanke hukunci

Hukumar zaben Najeriya ta dakatar da yunkurin yi wa Sanata Dino Melaye, mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, kiranye daga majalisar dattawan kasar.

Hukumar ta dakatar da yunkurinne bayan sanatan ya ki ya karbar takardar sanarwar fara tantance wadanda suka kada kuri’ar cewa suna son a yi masa kiranye daga mazabarashi.

Wata sanarwa da INEC ta fitar ta ce ya kamata a fara yi wa sanatan kiranye ne a ranar 3 ga watan Oktoba bisa sabon jadawalin da ta yi bayan kotu ta yi wasti da bukatar sanatan na dakatar da kiranyen.

Sai dai kuma kotun ta bai wa hukumar umarnin mika wa sanatan sanarwar kiranyen hannu da hannu, tare da bashi takardun da ke da alaka da yunkurin yi mishi kiranyen akalla mako biyu kafin a fara kiranyen.

Sanarwar hukumar ta ce jami’an hukumar tare da wani jami’in babban kotun tarayyar Najeriya sun je gida da ofishin sanatan sau shida, amman sun sami ofishinshi a kulle kuma ba su samu shiga gidansa ba.

  • Ko wane irin aiki ne ke gaban INEC?
  • Nigeria: Babu shakka digirina takwas — Dino Melaye

Har wa yau sanarwar ta ce sanatan ya ki karbar takardun a gaban ‘yan jarida bayan ‘yan majalisa sun koma bakin aiki.

Hukumar ta ce ta garzaya kotu domin a bata izinin sanar da sanatan game da kiranyen ta wata kafa ta daban.

Amman kotun ta ce hukumar ta sake komawa ta yi kokarin bai wa sanatan sanarwar fara kiranyen hannu da hannu.

Da ta kasa mika mishi sanarwar, sai hukumar ta sake koma wa kotun wadda ta ce ba ta da hurumi kan lamarin domin sanatan ya riga ya daukaka kara.

Domin ta kasa sanar da sanatan game kiranyen, hannu da hannu, hukumar ta ce ya zama dole ta dakatar da shirin har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan kararar da sanatan ya shigar.

A baya dai hukumar ta karbi sunayen jama’ar da suka sanya hannu a yunkurin tsige Sanata Melaye daga mazabarsa.

Sai dai babu wani cigaba sosai da aka samu tun bayan nan saboda an gabatar da batun a gaban kotuna daban daban.

Sanata Melaye ya yi watsi da yunkurin yana mai cewa bi-ta-da-kullin siyace ne kawai ake yi masa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *