Ko kun san sirrin mallakar miji?

Kunshi na daya daga cikin adon da mata kan yiwa mazajensuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKunshi na daya daga cikin adon da mata kan yi wa mazajensu

A birnin Kano da ke arewacin Najeriya, wasu mata sun dukufa wajen koya wa takwarorinsu matan aure da budurwai da zawarawa hanyoyin gyaran jiki da kara dankon soyayya tsakanin ma`aurata.

A baya-bayan nan dai masana na ganin cewa rashin iya kissa na cikin matsalolin da ke sanadin mutuwar aure a kasar Hausa.

Bisa al`ada ba kasafai mata kan fito fili su tattauna a kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure ko soyayya ba.

Malama Khadija Muhammad da aka fi sani da Mar`atus Saliha, wato Mace Tagari, na daga cikin matan da suke koya wa matan iya kissa da gyaran jiki, har ma da yadda mace za ta nuna wa mijinta tsagwaron.

Ta ce, babban burinta shi ne ta ga mata sun san sirrin zamantakewa ta aure, wanda ta ce idan babu wannan a aure to gaskiya akwai matsala babba.

Malama Khadija, ta ce daga cikin abubuwan da take yi akwai nuna wa mata illar zuwa wajen bokaye domin shirka ce, maimakon haka, ya kamata matan su rinka yin duk wani abu da suka san namiji zai bukata na zamani.

Don haka ta ce, sai mata sun cire kunya da ganda da girman kai da kuma jahilci, idan suna son su samu nasarar zama lafiya a dakunansu na aure.

Malamar ta ce, kowacce mace mijinta kwai ne a wajenta, don haka dole ta zage damtse wajen tarairayarsa ta hanyar iya kalamai masu dadi da kwalliya da tsafta da girmamawa da kuma uwa uba iya girki.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *