Yan hamayya sun yi barazanar kin shiga zaben Kenya

News
Raila OdingaHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionRaila Odinga ya ce har yanzu ba a yi sauyin da yake so ba

Shugaban ‘yan hamayya a Kenya Raila Odingaa ya ce ba zai shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a yi ranar 17 ga watan Okotoba ba “ba tare da an ba shi tabbacin samun kulawa ta shari’a da tsarin mulki” ba.

Ya ce dole a bi doka da kuma kundin tsarin mulki kasar.

A makon jiya ne kotun kolin kasar ta soke zaben da aka yi a watan Agusta, tana mai cewa hukumar zaben kasar ba ta bi kundin tsarin mulki wajen yin zaben ba.

Kotun ta bayar da umarni a gudanar da zaben ranar daya ga watan Nuwamba.

A zaben da aka yi ranar takwas ga watan Agusta, an ayyana Shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe shi da kashi 54 cikin 100, yayin da Mr Odinga ya samu kashi 45, a cewar hukumar zaben.

Mr Odinga ya shaida wa ‘yan jarida cewa dole a gudanar da sabon zaben ta yadda za a gyara dukkan kuskuren da ya taso.

“Mun san abubuwan da suka faru a zabukan da suka wuce, mun san abin da hukumar zabe ta yi kuma mun san cewa idan muka sake shiga zabe a wannan yanayi ba za a samu wani bambanci ba shi ya sa muka ce ba za a yi zabe ranar 17 ga watan Oktoba ba,” in ji shi.

Mr Odinga ya soki hjukumar zabe saboda sanya sabuwar ranar zaben yana mai cewa ba a tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar zaben ba.

Ya yi zargin cewa jam’iyyar Jubilee mai mulki ce ta sanya ranar sake zaben.

Ranar Litinin ministan Ilimi Fred Matiang ya bukaci hukumar zaben ta sanya ranar da za a sake zaben kafin 17 ga watan Oktoba domin guje wa cin karo da ranar da za a yi jarrabawar makarantu ta kasa baki daya.

odinga supportersHakkin mallakar hotoAFP
Image captionMagoya bayan jam’iyyar hamayya sun yi murnar soke zaben.
BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.