Rasuwar Kanti Bello asara ce ga Najeriya-Atiku

Rasuwar Kanti Bello asara ce ga Najeriya-Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ce mutuwar Sanata Kanti Bello asara ce ga fafutukar da Najeriya take yi wajen kafa damokradiyya mai dorewa.
A sakon ta’aziyyar da ya aike wa iyalai da kuma gwamnatin jihar Katsina ta hannun Ofishin Yada labaransa a Abuja, Alhaji Abubakar ya bayyana cewa ’yan Najeriya ba su taba mantawa da gudunmawar da marigayin ya bayar  wajen kafa damokradiyya a kasar nan ba.
Ya ce daya daga cikin halayen marigayin shi ne yadda yake fadar albarkacin bakinsa tare da bayyana ra’ayinsa a kowane lokaci.
“Dukkanmu iyalan gidan siyasar ’Yar’aduwa ne mun fara tun daga jam’iyyar  PFN zuwa SDP har zuwa PDP. Mutum ne mai kuzari kuma dan jam’iyya na kwarai”. Inji shi.
Sanata Kanti Bello da ke wakiltar mazabar Daura da ke jihar Katsina daga shekarar 2003 zuwa 2011 ya rasu da safe a ranar Talata a garin Abuja.
Wata majiya da ke kusa da marigayin ta bayyana cewa ya rasu yana dan kimanin shekaru 72 a duniya.
Aminiya

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *