Shugaba Buhari ya karbi rahoto kan Babachir

News
Buhari da OsinbajoHakkin mallakar hotoOFFICE OF VICE PRESIDENT
Image captionMataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya mikawa Shugaba Buhari rahoton

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi sakamakon binciken da aka gudanar kan zargin almundahana da ake yi wasu manyan jami’a gwamnatinsa biyu a ranar Laraba.

A watan Afrilu ne dai shugaban ya umarci wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakinsa ya binciki sakataren gwamnatin kasar da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA, bayan dakatar dasu bisa zarge-zarge daban-daban na almundahana.

Sai dai a bangare guda fadar shugaban ta sanar da dage zaman majalisar ministoci da ya kamata ya shugabanta a yau a karon farko cikin watanni da dama.

  • Babachir ya gana da Osinbajo, Shugaban NIA ya kasa ganinshi
  • Buhari ya dakatar da Babachir da shugaban NIA
  • Nigeria: Abin da ya sa Buhari bai hukunta Babachir tun farko ba

Tun a ranar 8 ga watan Mayu ne aka shirya shugaban kasar zai karbi rahoton amma sai rashin lafiyarsa ta hana hakan, inda ya koma Landan don ganin likita ranar 7 ga watan Mayu.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *