Yadda tsananin kadaici ke juya kwakwalwa

Health

Kwakwalwar Sarad Shourd ta fara juyewa bayan an tsareta a kurkuku tsawon wata biyu. Ta rika jin takun sawun fatalwa da walkiya na haskawa, inda a mafi yawan kwanaki take shafe yini a sunkuye tana saurare ta kafar kofa.

A wannan yanayin zafin, wannan mata ‘yar shekara 32 ta yi hawan tsauni tare da kawayenta a tsaunukan Kurdistan da ke kasar Iraki, a daidai lokacin da sojojin Iran suka kama su, bayan da suka kauce suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Iran.

An zarge su da leken asiri, inda aka tsare su a wani kebabben kurkuku da ke Evin a Tehran, ko wannensu a tsukukun daki. Ta yi juriyar kadaici na tsawon sa’a 10,000 ba tare da hulda da mutane ba kafin a saketa. Babban tashin hankalin da ta tasirantu da shi, shi ne rudanin tunani.

“A barin da nake hange, sai na fara ganin walkiyar haske, da zarar na janye kaina sai in ga babu komai, kamar yadda ta rubuta a jaridar New York Times a shekarar 2011.

“A wani lokacin, na kan ji kara, kuma babu wani abu, har zuwa lokacin da na ji hannun daya daga cikin masu gadin da ke tausaya mani a fuskata, yana kokarin farkar da ni sai na gane cewa hargowar duk tawa ce.”

Muna son kadaicewa a wasu lokuta, don kauce wa bukatun abokan hulda ko damuwar taron mutane. Sai dai ba kadaicewar mutum kadai ba, a wajen mafi yawan mutane tsawaita kebanta daga cikin al’umma kwata-kwata ba shi da kyau, musamman ga kwakwalwa.

Mun san wannan ba ma daga rahoton mutane irin su Shourd wadanda suka taba samun kansu a irin wannan hali ba, kai har ma daga gwaje-gwajen tantance tasirin kwakwalwa kan dabi’u kan killacewar kadaici da tauye kafofin ji da gani da shaka, wadanda aikinsu kan samu matsala saboda tsananin tunkarar harbutsattsun al’amura.

Me ya sa kwakwala ke kwarkwancewa da gaske idan mun kadaice a kashin kanmu, shin ko akwai dabarar shawo kan matsalar?

(Flickr/Cyri)Hakkin mallakar hoto(FLICKR/CYRI)
Image captionA cikin kurkuku, kadaici kan haifar wa kwakwalwa mummunan rudu

Muna sane da cewa a wani dan tsakani killacewa na da illa garemu. Wadanda aka tsananta musu kadaici suna da matsanancin hawan jini, kuma za su iya kamuwa da cuta, sannan akwai yiwuwar su kamu da cutar toshewar kwakwalwa da mantuwa.

Kadaici na iya hargitsa harkokin yau da kulum, kamar abin da ya shafi tsarin barci da fuskantar abin da mutum yake yi da wayau da furta managartan kalamai. Tsarin da ke haifar da wadannan al’amura har yanzu ba a tantance shi ba, ko da yake abin da ake kira kebanta daga mutane na iya illata garkuwar jiki.

Inda sinadaran dugunzumar damuwa da zafin ciwo ke kwararowa, ta yiwu irin hakan ya faru ga magabatanmu sa’adda suka kebanta daga gungun mutane sun jefa kansu a hadari na zahiri, amma matsalar ta fi illa a garemu.

Mafi yawan illolin kadaici sun fi tasiri a kwakwalwa. Ga wadanda suka fara, kadaici na rikita mana fahimtar lokaci.

Daya daga cikin mafi rikicewar lamurran shi ne ‘jinkirta lokaci’ kamar yadda wasu suka ruwaito, wadanda aka kebe su a karkashin kasa babu hasken rana.

A shekarar 1961, masanin kimiyyar albarkatun kasa dan Faransa, Michel Siffre, ya jagorancin zugar masu bincike a karkashin tsaunin kankara na makonni biyu, a karkashin tsaunin Alps, inda ya karke da zama har tsawon wata biyu, saboda sha’awarsa ta son fahimtar yadda duhu ke da tasiri a rayuwar mutum.

Sai ya yanke wa kansa watsar da abin da yake lura da shi ya koma “zama kamar dabba.” Lokacin da yake gwaje-gwaje da rukunin mutanensa, sun gano cewa ya kan shafe mintuna biyar kafin ya kirga abin da yake ganin kamar dakika 120 ne.

Kwatankwacin irin wannan na “rage tafiyar lokaci’ Maurizio Montalbini ya kawo rahoton wani masanin zamantakewar al’umma, mai matukar sha’awar kutsawa cikin kogo.

A shekarar 1993, Montalbini ya shafe kwana 366 a karkashin kasa a kogo kusa Peszaro a kasar Italiya, wadda aka tsara wa cibiyar binciken sararin sama ta NASA don motsa karsashin cillawa sararin samaniya, inda ya kafa tarihi a duniya kan yawan kwanakin da ya shafe a karkarshin kasa.

Da fitowarsa sai aka nuna masa cewa kwana 219 kawai ya yi. Barcinsa da farkawarsa sun kusa rubanyawa.

Tun daga nan masu bincike suka gano cewa a cikin duhu mutane na yin juyin sa’a 48: sa’a 36 na harkoki da sa’a 12 na barci ke biye masa.. Har yanzu ba a tantance dalilin hakan ba.

Getty/ImagesHakkin mallakar hotoGETTY/IMAGES
Image captionBayan fitowa daga zaman mako tara a karkashin kasa cikin duhu, Michel Siffre ya zame masa dole ya sanya madaurin kariyar ido

Sannan tsarinsu na jinkirta lokaci, Siffre da Montalbini sun ruwaito cewa akwai lokutan da suke samun rashin natsuwa a kwakwalwa. Sai dai wadannan matsalolin ba su da wata illa idan aka kwatanta da tsananin karawar tauyen kafofin ji da shaka na gwajin da aka yi a tsakiyar karni na 20.

A tsakanin shekarun 1950 da 1960, an baza jita-jitar cewa kasar Sin na amfani tsarewar kadaici ta “jirkita tunanin” fursunonin Amurka da ta kama a yakin Koriya da Amurka da Gwamnatin Canada duk sun zaku da kwata irin hakan.

Sashen tsaronsu sun bayar da tallafin kudi don gudanar da bincike kan shirin da a zahiri kumbiya-kumbiyar makirci ce da ba ta dace ba a halin yau.

Aiki mafi yawa an yi shi ne a Cibiyar aikin likitanci ta Jami’ar McGill da ke Montreal, a karkashin jagorancin masanin tantance tasirin aikin kwakwalwa ga dabi’u Donald Hebb.

Masu binciken McGill sun gayyato ‘yan sa-kai da aka biya su aka bibiyi kadin lamarinsu, wadanda daukacinsu daliban kwaleji ne da suka shafe kwanaki ko makonni a kashin kansu a bukkokin da rufinsu ba ya kara, aka yanke musu hulda da mutane.

Manufar ita ce a rage musu kaifin fahimta, ta yadda za a ga yadda za su kasance da irin dabi’unsu bayan babu abin da ya faru. An rage ji da gani da saurare da tabawa, aka kare su da gilashi da ake iya hango su, amma su ba sa ganin kowa a sanya musu safar auduga daure da kwali har zuwa kan yatsu.

Kamar yadda Mujallar masana kimiyyar Amurka ta ruwaito a lokcin, an sa sun kwanta a kan matasai don takaita karar motsi, sannan an sanya na’urar sanyaya wuri mai sarrafa kanta don dode dundumin kamar kara.

Bayan sa’o’i kadan, sai daliban suka dugunzuma cikin rashin kwanciyar hankali. Sai suka fara neman abin da zai zaburar da su magana da waka ko baitukan wake a kashin kansu don shawo kan damuwar kadaici.

Bidiyon gwajin kebancewar kadaici na BBC Horizon da aka gudanar.- ka karanta dimbin bayanai game da shirin.Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionBidiyon gwajin kebancewar kadaici na BBC Horizon da aka gudanar.- ka karanta dimbin bayanai game da shirin.

Tauye kafofin ji-gani-shaka-da saurare na iya haifar da rudanin kwakwalwa wani lokacin ta yi tsororuwar kusurwowi (geometric shapes) ko nuni ga haske da sabunta komai ya zama bako.

Al’amari mafi tayar da hankali shi ne rikicewar kwakwalwa. Su kan fara da nunin haske da layuka ko siffofi, sai kawai su karke a cikin yanayin hargitsin harbutsutsai, kamar kurege yana kai-kawo da buhuna a kafadarsu ko jerin tabarau barjak a kan titi.

Babu abin da za su iya yi kana bin da suka gani; wani mutum in ya ga karnuka kawai; wani kuwa jarirai.

Wasu da suka samu jin sauti a rudanin kwakwalwarsa; kayan kida da jerin mawaka. Sauran sun ji kamar an taba su; wani mutumin ya ji kamar an kwada masa dan dutse da aka harbo daga bindiga.

Wani kuwa zuwa ya yi ya rika kokari kama hannu kofa, yana jin kamar wutar lantarki ta ja shi.

Da suka fito bayan an kammala gwaji, sun sha matukar wahala kafin su warware daga jirkicewar kafofin ji-gani-da-saurare zuwa zahirin gaskiya, amma tuni su sun yarda cewa dakin da suka kasance yana motsawa, ko abubuwan da suke gani suna sauya kamannu da girma.

Dugunzumar damuwa

Masu binciken sun so ganin wadan da suka bi kadin lamarinsu a tsawon makonni, amma sai aka dakatar da gwajin saboda sun tagayyar ta yadda ba za a iya ci gaba ba. Kadan ne daga cikinsu suka jure har kwana biyu, amma bnabu wanda ya kai mako guda.

Bayan kammalawar, Hebb ya rubuta a Mujallar masana tasirin aikin kwakwalwa kan dabi’u cewa sakamakon sun kasance “masu matukar rashin tabbas garemu… wani abu ne daba na ji cewa ‘Yan Sin na jirkita kwakwalwar fursunoni a wani yanki na duniya; wani lamari ne da za ka bincika a dakin bincikenka, cewa, gusar da gannai da jin sauti da yin mu’amalar taba jiki a tsakanin lafiyayyaun daliban jami’a na kwanaki kadan ya girgiza shi, har zuwa kasa.”

A shekarar 2008, Likitan tantance tasirin aikin kwakwalwa kan dabi’uIan Robbins recreated Hebb ya yi gwajin hadin gwiwa da BBC, inda aka kebe mutum shida da suka kansu a dakuna marasa kara tsawon sa’a 48 a tsohuwar mafakar nukiliya ta karkashin kasa.

Sakamakon dai irin daya ne. ‘Yan sa-kan da aka bi kadin lamarinsu sun duguzuma cikin damuwa da matsanancin sosuwar zuciya da tsoro da hargitsewar aikin kwakwalwa.

Sun kuma samu rudun da ya haifar musu ganin: kwasfan kwai 5,000 da maciji da jakin dawa da kananan motoci; dakin ya fara tashi; sauro; jiragen yaki na shawagi.

Akwai ci gaban binciken da za mu kawo nan gaba.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.