Daukacin mayankar Abuja suna cikin mummunan yanayi – Bincike

Daukacin mayankar Abuja suna cikin mummunan yanayi – Bincike
Wurin da ake ajiye dabbobi su huta kafin a yanka a mayankar Karu, inda yanzu ya zame masu makasa. Hotuna daga Adam Umar

Mayankar dabbobi hudu da ake da su a Abuja wadanda aka fara amfani da su lokacin mulkin soji na Janar Ibrahim Babangida sama da shekara 30 da suka gabata suna fama da rashin inaganci ko kayan aiki da tsoffafin gine-ginen da aka jima ba a gyara su ba.

Binciken da Aminiya ta gudanar a mayanka hudu da ake da su a garuruwan Karu da Kubwa da Gwagwalada da Abaji da kuma wata ta ’yan kasuwa mai zaman kanta da ke garin Deidei da a a gina daga baya, ya gano duk suna fama da tarin matsaloli da suka hada da rashin ruwan gudanar da aiki da lalacewar kananan magudanun ruwan da suke daukar ruwan da aka yi amfani da shi ko jini zuwa inda aka tsara da rashin na’urorin sanyi don adana naman da ya yi kwantai, sai kuma faduwar katanga da ke ba barayi damar sace dabbobin jama’a.

Binciken da Aminiya ta gudanar a daukacin wuraren yanka dabbobi na Abuja da suka hada da wasu kananan mayanka da suke garuruwan Bwari da Zuba da Dutsen Alhaji da Karmo da Gwagwa da Karshi da Kuje da wasu kananan wuraren yanka a garuruwan Lugbe da Dobi da Anagada da Paikon Kore da kuma Kabusa, ya gano cewa rashin ruwan gudanar da aiki wanda ya shafi daukacin wuraren yankan in ban da na garin Kubwa da ke da ruwan famfo da na Deidei da ke da rijiyar burtsatse, sauran sun dogara ne da sayen ruwa daga ’yan garuwa, kuma hakan yana sa suna yin tsumulmulan ruwan wajen tsabtace wuraren.

A garuruwan Gwagwa da Lugbe da kuma Kuje wasu ma’abota wajen sun shaida wa wakilinmu cewa suna amfani ne da ruwan rafi da ke da kusanci da wuraren domin wanke nama da kuma wuraren yanka a lokutan damina.

Binciken ya gano cewa sama da rabin fulotin manyan wuraren yankan, tuni an gina gidaje a cikinsu, sakamakon cuwa-cuwar sayar da fulotan da ake zargin wadansu tsofaffin daraktoci daga sashin kula da noma na Ma’aikatar Birnin Tarayya suka yi a baya.

Sauran matsalolin da suke addabar wuraren yankan sun hada da rashin gidajen likitocin dabbobi a wuraren yankan domin tantace lafiyar dabba kafin a yanka ta da kuma bayan an yanka kamar yadda tsarin wuraren ya nuna, inda ake fara yanka bayan idar da Sallar Asuba a kullum.

Sannan  akwai matsalar rashin motoci masu na’urorin sanyi domin safarar nama daga wuraren yankan zuwa kasuwannin birni da kewayen Abuja kamar yadda ake yi a Jihar Legas, kamar yadda mahautan suka koka. Maimakon haka ana amfani da budaddun motoci ne ko babura ko kuma baro-baro wajen safarar naman.

Sauran matsalolin sun hada da amfani da taya wajen babbakar dabbobi, kamar awaki, wanda hakan ke ke jawo gurbacewar muhalli da yanayi da kuma cutar da makwabtan wuraren.

Wadansu shugabannin mahauta da Aminiya ta zanta da su sun yi korafin cewa dangantakarsu da gwamnatin Abuja a yanzu ba ta wuce amsar haraji daga dabbobin da suke yankawa a kullum ba.

Jadawalin yanka dabbobi a wuraren ya nuna a kullum ana yanka shanu kimanin 200 a mahautar Karu, 120 a Deidei, 40 a Kubwa, 35 a Gwagwalada, 8 a Abaji, 30 a Bwari, 25 a Kuje, 12 a Kwali, 10 a Dutsen-Alhaji. Sauran su ne 30 a Lugbe, 18 a Karmo, sai kuma 30 a Gwagwa, kuma ana biyan harajin Naira 800 ga jami’an gwamnati a kan kowace saniya daya da aka yanka, in ban da na Deidei mai zaman kansa, wanda dan kasuwa ne da ya gina yake karba.

Haka Aminiya ta gano cewa ana yanka awaki ko tumaki kimanin 600 a duk wuni a mayankar Karu, 2000 a Deidei, 70 a Gwagwalada, 40 a Abaji, 70 a Bwari, 50 a Kuje, 20 a Kwali, 40 a Dutsen Alhaji, 10 a Lugbe, 70 a Karmo da 30 a Gwagwa, inda ake biyan harajin  Naira 100 a kan kowace akuya ko tunkiya.

Sakamakon zargin watsi da bukatun mahautan duk da harajin da suka ce suna biya a kullum, mahautan sun bukaci gwamnati ta sayar musu da wuraren yankan domin inganta su tare da samar musu da abubuwan da suke bukata.

Shugaban kungiyar Mahauta ta Abuja, Malam Aminu Lawan Bakin-ruwa ya ce mambobinsu a shirye suke su rika biyan gwamnati duk abin da ta dora musu a shekara tare da bin sharrudanta sau-da-kafa muddin aka mika musu kula da wuraren, maimakon barinsu a hannun manajojin gwamnati, wadanda ya ce babban burinsu shi ne amsar haraji maimakon inganta su.

Baya ga shanu 558 da ake yankawa a wuraren yanka na Abuja da awaki ko tumaki kimanin 3000 a duk wuni, akwai kuma karin dabbobin da manyan garuruwa biyu da ke makwabtaka da Abuja kamar Suleja a Jihar Neja inda ake yanka shanu kamar 250 a wuni da awaki ko tumaki 100. Bayanai sun ce kimanin kashi 75 ciki 100 na abin da ake yankawa a Suleja na karewa a kasuwannin Abuja. A garin Mararaba da ke Jihar Nasarawa kuma ana yanka shanu kimanin 50 da awaki 300 a duk wuni sannan kimanin kashi 60 cikin 100 na namansu ke shigowa Abuja.

aminiya

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *