Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Venezuela

News
Shugaba Donald Trump a tsakiyaHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionVenezuela dai ta ce akwai bukatar bukatar Amurka ta daina tsoma bakinta cikin al’amurran cikin gidanta

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce bai kau da yiwuwar daukar matakin soji wajen yin maganin rikicin siyasar Venezuela.

Da yake magana da manema labarai a New York, ya bayyana Venezuela a zaman makwabciyar Amurka inda mutane ke shan bakar wahala kuma suke mutuwa.

Mr. Trump ya ce Amurka na da dakaru a fadin duniya, da suka hada da wurare masu nisa wadanda Venezuela ba ta kai nisan su ba.

Dama dai dangataka tsakanin Venezuela da Amurka ta yi tsami inda har a makonnin baya gwamnatin Trump ta saka wa wasu manyan jami’an gwamnatin kasar takunkumin shiga Amurka ciki har da Shugaba Maduro.

Yanzu kuma da Mr. Trump ya ce Amurka na da hanyoyi da yawa na magance matsalar kasar ta Venezuela ciki har da daukar matakin soji, zaman tankiyar ya kara hauhawa.

  • Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi
  • An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka
  • Mutane uku sun mutu a boren Venezuela

Ministan watsa labaran Venezuela, Enesto Villegas, ya mayar da martani da cewa kalaman Mr. Trump su ne kalamai mafiya tsauri kuma na rashin dattako da aka taba furtawa kan kasarsa.

Yayin da shi kuwa Ministan tsaron kasar Vladimir Padrino ya ce kira kalaman na Trump da aikin hauka da kuma tsatsauran hali na koli.

Fadar White House ta fitar da sanarwa cewa Shugaban Venezuelar Nicola Maduro ya nemi yin magana da Shugaba Trump ta wayar tarho kuma shugaban zai amince ya yi magana da shi, da zarar an mai do da tsarin dimokradiyya a Venezuela din.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.