Kasuwar hannayen jari ta Nigeria ta yi matukar bunkasa

News
Yadda ake hada-hada a kasuwar hannayen jarin NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA watan Afrilu ne dai CBN ya yanke shawarar barin kasuwa ta yi halinta wajen sayar da kudaden musaya na kasashen waje ga kamfanonin kasar

Darajar kasuwar harkokin hannayen jari ta Najeriya na ci gaba da karuwa bayan ta samu bunkasar da ba ta yi kamarta ba a wata 33 da suka wuce ranar Talata.

Zuwa lokacin da aka rufe kasuwar ranar Laraba, darajar ta karu da kashi daya da digo ashirin da shida cikin dari idan aka kwatanta da ranar Talata. Wato yawan hada-hadar da aka yi ta karu daga 37,525.38 zuwa 37,999.56.

Kwana shida kenan a jere darajar kasuwar na hauhawa, sakamakon daidaiton da aka samu a kasuwar musayar kudaden kasashen waje, da kuma ribar da manyan kamfanonin kasar wadanda ake hada-hadar hannayen jarinsu suka rika samu a wata shida da ya gabata.

“Wasu tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnati ta yi, musamman ta fuskar samar da kudaden musaya na kasashen waje, wadanda suka bai wa kamfanoni damar shigo da injina sun taimaka wajen haifar da wannan kyakkyawan sakamako”, inji Malam Abubakar Aliyu, wani mai ruwa da tsaki a kasuwar.

Wadannan tsare-tsare ne dai suka karfafa gwiwar masu zuba jari na kasashen waje suka fara dawowa kasuwar don a dama da su.

A watan Afrilu ne dai Babban Bankin Najeriya ya yanke shawarar barin kasuwa ta yi halinta wajen sayar da kudaden musaya na kasashen waje ga kamfanonin kasar, lamarin da ya sa dalar Amurka ta wadata.

Shekara uku ke nan masu zuba jarin na kasashen waje na kaurace wa kasuwar.

  • Dangote ya sayar da hannun jari mai yawa
  • Nigeria: Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’
  • Samun Dangote na yini zai ciyar da talakan Nigeria a shekara

A makon jiya ne dai Rukunin Kamfanonin Dangote, wato Dangote Industries, ya sayar da hannayen jarinsa miliyan 416 na kamfanin siminti na Dangote, wato Dangote Cement, a kan kudi naira biliyan 86 (kwatankwacin dala miliyan 236) ga wasu masu zuba jari na kasashen waje.

A cewar Malam Abubakar Aliyu, wannan ya taimaka sosai ba kawai wajen daga darajar jarin Dangote Cement ba, har ma da sauran kamfanoni: “Wannan ya taimaka wa kasuwa, kuma ya taimaka wa kasa, don ranar da maganar ta fito darajar hannayen jarin kamfanin ta tashi sosai.

Birnin Lagos ne cibiyar hada-hadar kasuwanci ta NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Hakan ne ya sa darajar hannayen jarin wasu kamfanonin ma ta tashi”.

Baya ga kamfanin na Dangote Cement, wasu kamfanonin da suka bunkasa a kasuwar, wadanda su suka fi karfin jari, su ne Dangote Flour, da Nestle, da Nigerian Breweries, da Guinness Nigeria, da Cadbury.

A baya dai masu zuba jari na kasashen waje ne ke da mafi tsoka na hannayen jarin kasuwar, kuma janyewarsu na cikin abubuwan da suka haddasa rudani. Shin ko akwai fargabar za a iya komawa gidan jiya?

“In ka ga {faruwar hakan}”, in ji Malam Abubakar Aliyu, bayan ya yi wata ‘yan guntuwar dariya, “ta danganta da shirye-shiryen da aka yi a kasa. Ko da yau din nan in gwamnati ta fitar da wasu tsare-tsare da {masu zuba jarin} suka ga cewa ba za su amfane su ba, ficewa za su yi”, sannan ya kara da gargadin cewa, “yanzu ya rage wa gwamnati, ta ga cewa tsare-tsaren da take yi suna aiki…amma in ta yi wani abin da zai tsoratar da masu zuba jari dole za su kwashe kudinsu su fita”.

Kasuwar hadahadar hannayen jari ta Najeriya dai ta dade tana tangal-tangal sakamakon matsalar tattalin arzikin da kasar ta fada, sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya da karancin kudaden musaya (duba alkaluman da kasuwar ta fitar a hoton da ke kasa).

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.