Gwamnatin Kaduna ta ce sojoji sun kashe ‘yan bindiga 50 a dajin Birnin Gwari

Hausa

Sojoji

Getty ImagesCopyright: Getty Images

Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa an kashe ‘yan fashin daji sama da 50 a wani ruwan wuta ta sama da aka yi a yankunan Saulawa-Farin Ruwa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar.

Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya shaida haka a wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sanarwar, wannan ya biyo bayan hare-haren da gwamanti ta kaddamar na hadin-gwiwa.

Sojojin sama sun yi shelar wuta da taimakon na kasa a yankin Dogon Dawa-Damari-Saulawa, a cewar sanarwar.

Sannan sanarwar ta kuma shaida cewa an kona tarin makamansu da baburar da suke amfani da shi.