Shugaba Buhari ya taya Yakubu Gowon murna cika shekaru 87 da haihuwa

Hausa

Buhari da Gowon

VanguardCopyright: Vanguard

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar na soji, Janar Yakubu Gowon murnar cika shekaru 87 da haihuwa.

Buhari ya ce yana wa tsohon shugaban fatan alheri da yawan shekaru masu albarka cikin koshin lafiya.

A wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari ya fitar, Malam Garba Shehu na yabawa Yakubu Gowon bisa rawar da ya taka wajen ci gaban Najeriya, da kuma gudunmawarsa wajen tabbatuwar zaman lafiya da hadin-kai.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba za ta taɓa mantawa da kyawawan ayyukan da Gowon ya kawo ko ya aiwatar ba, kamar samar da shirin yiwa kasa hidima na NYSC a shekarun 1970, kirkirar sabbin jihohi da manyan ayyuka da yau ake alfahari da su.

BBC HAUSA