Gomna Tambuwal yayi kakkausan martani ga FFK bayan ficewar sa daga jamiyyar PDP zuwa APC da yayi.

Politics

Gomnan jihar Sokoto Rt. Aminu Waziri Tambuwal yace duk da femi-fani-kayode baida muhimmanci sosai lokacin da yake cikin jamiyyar PDP amma baiga wani abin azo a gani da jamiyyar APC tayi ba harda zaija hankalin FFK ya koma APC bamuji dadin ficewar sa daga PDP ba zuwa jamiyyar da ta kada Yan Nigeria cikin wani yanayi na tsadar rayuwa.

Jaridar Sokoto Online ta ruwaito cewa gomnan yace ko a shekarar 2019 da ta gaba ta sai da muka gargadi yan Nigeria da cewa kada su kus kura su sake zabar jamiyyar APC amma duk da haka sai da suka zabe ta, yau ga bala’in da suka fada a cikin.

Kana kuma gomna Tambuwal yayi gargadi wa tsohon shugaban kasa Good Luck Jonathan da cewa kada ya kus kura ya koma jamiyyar APC wacce ake rade-raden zai koma kamar yadda Sokoto Online ta ruwaito.

Tambuwal ya kuma yi gargadi wa shugaba Buhari cewa kada ya kus kura ya tsayar da Jonathan takara a zaben 2023 dake tafe idan ya koma APC.

Domin kuwa a cewar gomnan Jonathan din da ya sani har yanzu bai canza ba jaridar Sokoto online ta ruwaito.

Illela Daily Post