Wauta ne sake ciyo wa ƴan Najeriya bashi – Obasanjo

Hausa News
  1. Oluseagun ObasanjoCopyright: Oluseagun ObasanjoTsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya mayar da martani ga shirin shugaba Muhammadu Buhari na karbo sabbin rance, yana mai cewa yin aro don tara bashi ga ƴan gobe babban laifi ne.Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a gefen wani taro a Afirka ta Kudu, Obasanjo ya ce cin bashin da ake yi sannan ake kin biyan wanda ake bin kasar na iya zama gagarumar matsala ga gwamnacin da za su zo a gaba.Ko da yake ya ce cin bashi ba matsala bane, tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana cewa abin da zai iya zama matsala shine biyan bashin.”Idan ana ciyo bashi don aiwatar da ayyukan da za su iya biyan kudinsu ne to wannan ba matsala bane, in kuwa don aiwatar da ayyukan al’amuran yau da kullum ne to wannan babbar wauta ce” inji Obasanjo.Article share tools
  2. An wallafa a 9:309:30Koriya Ta Arewa ta yi tofin Allah-tsine ga sabon kawancen Amurka da ƙasashen TuraiKim Jong Un