Kungiyar masu ‘Adaidaita sahu’ ta Kano ta janye yajin aikin da ta shiga sannan ta bada umarni ga mambobinta da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban kungiyar, Mansur Tanimu ne ya tabbatar da haka a ranar Talata a tattaunawarsa da jaridar Aminiya ta wayar tarho.
Ya ce wannan hukuncin, sakamako ne na taron da aka gudanar da yammacin Talata tsakanin hukumar kula da ababen hawa ta Kano(KAROTA) da kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) sai kungiyar ta adaidaita sahu(Keke-napep).