NA SHIRYA TSAF DON FITAR DA MUTUN MILIYON 100 DAGA KUNCIN TALAUCI- INJI BUHARI

News
“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, burin gwamnatinsa na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci ba zai samu haka kurun ba, dole yana bukatar bin wasu mahimman hanyoyin da suka dace domin tabbatar da wannan buri.

Da yake magana a ranar Talata wajen taron majalisar shawartar shugaban kasa a kan tattalin arziki wanda mataimakain shugaban kasa, Yemi Osinbajo yake jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasa Buhari ya amince da shawarwarin majalisar wajen bin hanyoyin rage kangin talauci a cikin kasar nan tare da farfado da tattalin arziki.
Jam kadan bayan gabatar da rahoton na rage kangin talauci a cikin kasar nan, shugaban kasa Buhari ya bukaci kwamitin su gabatar da kundi ga majalisar zantarwa a matsayin hanyar bayar da shawara.
Haka kuma ya amince da burin majalisar na tsarin cire ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci wanda ya nuna cewa akwai tarin matsaloli amma za a samu nasarar shirin. Shugaban kasan ya yi mamakin yadda kasar nan ta shiga a baya, inda kasar take da dinbin dokiyoyi da za su rage kangin talauci gaba daya.
“Na firgita lokacin da na ji tasowar matsaloli a cikin kasar nan bayan muna da dinbin filayen noma wanda za a iya amfani da su wajen samun abinci. Mu godewa Allah a kan ni’imar da ya yi mana a kasar nan. Mun tabbata mana da abin da muke iya fitarwa,” inji shi.
Farfesa Doyin Salami ya hade jawabinsa da na shugaban kasa Buharim, inda ya ce za a gabatar wa ministoci baya domin su kaddamar da shirin a ma’aikatunsu a ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
Mista Salami ya bayyana cewa, wannan shirin ya samu amincewar masu ruwa da tsaki a dukkan fadin kasar nan kamar yadda mataimakin shugaban kasa da sakatarorin gwamnati a dukkan jihohi 36 da gwamnoni suka amince da shirin farfado da tattalin arziki, wanda za a yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da bankin duniya da asusun bayar da lamuni ta duniya da bankin bunkasa yankin Afirka da kungiyoyin fararen hula da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya yaba da yadda kasar nan ta fita daga cikin matsin tattalin arziki, amma ya yi gargadin a kara tashi tsaye wajen fadada ci gaban tattalin arziki ta hanyoyi da dama tun da dai kasar nan tana da danbin jama’a.
Shirin rake kangin talauci wanda aka gabatar yana bukatar fadada harkokin noma domin magance kangin talauci a fadinjihohin nan wajen tabbatar da dai-daita tattalin arziki wajen inganta kamfanoni a cikin kasar nan. Wannan shiri ya samu karbuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki da mashawarta daban-daban da kuma masu zaman kansu a lungu da sako da ke cikin kasar nan.
Kwamitin ya bayyana cewa, an samar da sababbin hanyoyin ga shirin wanda za a bi domin rage kangin talauci a cikin kasar nan. Ba rashin kudi ne kadai talauci ba. Talauci sun hada da karancin samun muhalli da lafiya da ilimi da ayyukan yi wanda dukkan su ake kokarin magancewa.
Lallai an yi yunkurin rage radadin talauci a cikin kasar nan wanda ba a taba ganin irin sa ba, majalisar mashawarta ta mika rahotonta a karon farko domin samun nasarar cimma wannan buri tare da gyara kurakuran da aka samu a baya, a karon farko an samu hada ra’ayin gwamnati da jihohi da masu zaman kansu da kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyin fararen hula.
Rage kangin talauci ba wai gwamnati kadai ya shafa ba, kowa yana da rawar da zai iya takawa. Majalisar ta bayar da shawarar da a shirya majalisar rage kangin talauci wanda zai hada da dukkan masu ruwa da tsaki, wanda shugaban kasa ya yi na’am da wannan shawara.

Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published.