Kungiyar Kwallon kafa Ta Neja Tornadoes Dake Minna Na Cikin Halin Ha’ula’i.

Sports

A wani Ruhuto Da Shirin Tsalle Daya Na Rediyo Prestige ya Tattara Na Nunar Da Yadda Wasu Yan’jihar Neja Ke Bayyana Takaicin Yadda Al’ammuran Kungiyar Kwallon kafar Ke Durkushewa.

Masu Korafin Na Zargin Shugaban Hukumar Tafiyar Da Kungiyar Adamu Aliyu Da kuma Mai Horas Dasu Coach Bala Da Babakere komai Na Kungiyar.

Ruhuton Ya Jiyo Wani Zargin Da Ake yiwa Shugaban Na Danne Hakkokin Yan’wasa Da kuma Yadda Mai Horaswan ke yin Kashe Muraba Da Yan’Wasa.

Sun Cigaba Da Yin Kira Ga Gwamnan Jihar Neja Daya Kaddamar Da Bincike A Kungiyar Wacce A Yanzun Take Gargarar Dusashewa.

Akwai Kuma zargin Cewa Kungiyar Taki Sayo Yan’wasa Duk da Kudaden Da Gwamnati Ta Bayar Na A Siyo Yan’wasan.

Yanzun Dai Kusan Shekaru Uku Kenen Da Kungiyar Ta Fada Rukunin Yan’ Inna Rididi.

Tsalle. Daya Prestige

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *