Assalam: Bala Lau ya ce sun samu taimako daga wajen wadanda ba Musulmai ba

Hausa

By Muhammad Malumfashi

Shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da jami’ar da su ke kokarin ginawa.

Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa al’umma ce gaba daya su ke daukar dawainiyar wannan jami’a bayan sun nemi a bada gudumuwar N1000.

Da ya ke hira da BBC Hausa, Shehin ya ce: “Har wadanda ba musulmai ba, mun ga sun aiko da kudi.”

Ko da mallakar Jami’ar As-Salam ya na hannun kungiyar JIBWIS ne, duk wanda ya cika sharudan zuwa jami’a, zai iya samun damar shiga makarantar.

KU KARANTA: Rade-radin mutuwa: Lauyoyin Sheikh Abdullahi Bala Lau sun yi magana

Da ya ke maganar abin da ya sa su ka kafa wannan jami’a, Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa za ta samar da sauki ga Musulmai da sauran ‘Yan Arewa.

Ya ce ana bukatar jami’a a yankin ganin yadda matasa miliyan biyu su ke rubuta jarrabawar JAMB duk shekara, amma a karshe 500, 000 su ke zuwa jami’a.

Bayan haka, Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa jami’ar za ta taimaka wajen rage shaye-shaye musamman a Arewa da ake da miliyoyin ‘yan kwaya.

Wata fa’ida ta gina wannan jami’a ita ce yakar ta’addanci da ilmi. Ya ce ana fama da kashe-kashe da zubar da jini da ta’adi iri-iri da sunan addinin islama.

Lau ya ce wannan jami’a da za a gina za ta canza tunani da ra’ayin masu barna da rigar musulunci.

Akwai dalibai da ke karatu a jami’o’in musulunci da ke kasashen Masar, Sudan da Saudi, amma su dawo gida babu wurin aiki, don haka aka kafa jami’ar.

Haka zalika ya ce akwai yaran da su ka yi karatun NCE da ke bukatar cigaba da karatu da karantarwa irin ta musulunci a irin wannan sabuwar jami’a.

Kun san cewa a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2020, aka kaddamar da shirin aikin gina jami’ar Assalam Global University a garin Hadejia, jihar Jigawa.

Gwamnoni biyar da wasu ‘Yan Majalisa sun taimakawa kungiyar da gudumuwar Miliyan 400.

Source: Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *