A rushe sanatoci don a rage kashe makudan kudade – Gwamna

News

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma gwamna Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa kamata ya yi a daina tsarin Majalisar Dattawa, domin a rage kashe kudaden gwamnati bagatatan.

Kayode ya nuna goyon bayan sa ga abin da rahoton Kwamitin Stephen Orosaye ya kunsa, wanda ya bada shawarar a hade hukumomin gwamnatin tarayya wadanda ayyukan su ya yi kama da juna, a wuri daya, domin a samu ingancin aiki da kuma rage kashe kudade.

Fayemi ya yi wannan jawabi ne a wurin taron Makomar Tattalin Arzikin Kasa, na 25 da aka gudanar a Abuja.

Gwamnan ya ce tsarin majalisa daya tilo ne ya fi dacewa da Najeriya, musamman a wannan yanayi na matsalar tattalin arzikin kasa.

PREMIUM TIMES a mokonni biyu da suka gabata ta buga labarin yadda Sanata Rochas Okorocha ya ce ya kamata a rage yawan sanatoci daga uku a kowace jiha, zuwa daya tilo daga kowace jiha.

Okorocha ya ce duk abin da sanata uku suka yi, to sanata daya ma zai iya yin sa. Sannan kuma ya ce su ma mambobin majalisar tarayya sun yi yawa, a maida su uku kadai daga kowace jiha.

Yayin da Okorocha ya yi korafin cewa kudaden da ake kashewa a Majalisar Dattawa da ta tarayya su na da matukar yawa, a wannan kasafin kudi na 2020, an kasafta cewa za a kashe naira bilyan 125 wajen gudanar da ayyukan tafiyar da Majalisar Tarayya.

Abin da Fayemi ya Dogara dashi

“Ni a gani na tsarin majalisa daya tilo ne ya dace da mu. Majalisar Tarayya ce aka fi bukata a tilas, domin su ne ke wakiltar jama’a.

“Amma ku duba ku gani. Sanata uku daga karamar jiha kamar Ekiti, sannan kuma duk girma da yawan al’ummar jihar Legas, ita ma wai sanata uku kadai.

“Kawai gani na ke gawa a rushe tsarin Majalisar Dattawa. Akwai abubuwa da dama da suka kamata a rushe cikin gwamnatin tarayya.”

Hausa premiuntimes

Leave a Reply

Your email address will not be published.