Budurwa ta hada baki da saurayinta ya yi wa kawarta fyade

News

Wata budurwa ‘yar shekaru 23 da ake zargi da hada baki da saurayinta ya yi wa kawarta fyade ta shiga komar ‘yan sandan jihar Ogun.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan DSP Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Aminiya cewa, yarinyar da aka yi wa fyaxen wacce aka sakaye sunanta ita ce ta shigar da kara ga rundunar ‘yan sandan tace a ranar Larabar makon jiya tana zaune a gida sai kawarta ta turo mata sako a manhajar wassaf ta wayar salula inda ta umarce ta da ta sayi abinci tana gidan saurayinta mai suna David Peremobowe, “ko da ta kaiwa saurayin abincin sai ya bata giya a kwalba da ta sha nan take jikinta ya mutu ta fita hayyacin ta sai ya yi amfani da wannan damar ya yi mata fyade yayin da kawarta mai suna Eniola Shittu ta dauki faifon bidiyon fyaden da wayar ta, mun kame ta tare da saurayinta da ta hada baki da shi ya yi wa kawarta fyaden”. In ji shi. Ya ce, Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Ogun Bashir Makama ya bada umarnin bincikar lamarin kafin a gabatar da wadanda ake zargin a kotu.

Aminiya daily trust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *