Za’a yi kitso da kwarkwata: EFCC ta dakatar da Buhari daga nada wasu mutane 5 minista

News

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa ta dakatar da duk wani shiri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na nada wasu mutane 5 mukamin ministoci a sabuwar gwamnatinsa. Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa EFCC ta dakatar da shugaban ne sakamakon bankado wasu makudan kudade da mutanen biyar suka mallaka, wanda hakan yasa hukumar ta lika musu alamar tambaya. KU KARANTA: Gwamnan jahar Bauchi ya sanar da nadin sabbin mukarrabansa guda 4 Binciken EFCC ya nuna cewa mutanen 5 suna da makudan kudade a asusun bankunansu, kuma wadannan kudade suna nan a naira da daloli ne, haka zalika binciken ya bankada wasu asusun mallakin mutanen dake bankunan kasashen duniya, musamman kasashen da suka yi suna wajen boye kudaden sata. Idan za’a tuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nanata burinsa na kokarin nada mutanen daya tabbatar da nagartarsu, kuma ya tabbatar da amincinsu a matsayin ministoci a sabuwar gwamnatinsa. Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin majalisun dokokin Najeriya a fadar Villa a ranar Litinin din data gabata, inda ya nemi yan Najeriya su yi hakuri dashi saboda baya so ya sake tafka kuren da yayi a baya wajen nada ministocin da bai sansu ba. A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta mika wani katafaren gida mai hawa 5 ga kamfanin muryar Najeriya, VON, EFCC ta kwace wannan katafaren gida ne daga wajen tsohon babban hafsasn hafsoshin Sojan Najeriya, marigayi Alex Badeh, wanda ya saya da kudaden sata.

hausa.legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *