Buhari Ya Dakatar Da Batun Samar Da Rugar Fulani

News

Biyo bayan korafe-korafe da wani ba’adin al’umma suka yi ta yi dangane da rugar Fulani ta zamani da gwamnatin Buhari ke shirin samarwa, Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shirin kamar yadda majiyarmu JARIDAR THISDAY ta ruwaito.
Shugaban Kasan, bayan jin ra’ayin masu ruwa da tsaki, ya cimma matsayar sake bibiyan lamarin domin samar da mafita ga rikicin Makiyaya da Manoma da ke ci gaba da afkuwa a wasu sassan Nijeriya.
Majiyarmu tamu ta ce, wannan bayanin ya fito ne daga majiya mai tushe daga fadar Shugaban Kasa, kuma nan kusa za a fitar da cikakkiyar sanarwa kan dakatarwar.

Leadership

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *