Abinda Tawagar Damina Su Ka Yi Cin Mutuncin Majalisar Dokokin Bauchi Ne – Dakta Ladan

Interviews News

DAKTA LADAN SALIHU shi ne kakakin gwamnan jihar Bauchi. A wata hira da ya yi da ‘yan jarida, ya shaida cewar, ballewa da tagawar su Hon. Kawuwa Damina su ka yi su ka ce sun sake yin zaben shugaban majalisar jihar bayan wanda majalisar ta gudanar, cin mutuncin majalisar jihar da ita kanta jihar ne a idon duniya. Ya fayyace yadda lamarin ya faru daga farko har karshe.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA, na cikin tawagar manema labaran da su ka dauki hirar. Ga abinda ya nado ma na: An samu tirkaniya a majalisar dokokin jihar Bauchi wanda har hakan ya sanya jama’a cikin shakku kan zaben kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi da aka ce Kakakin majalisar su biyu ne, me za ka ce?

Ina son na yi gyaran fuska kan wannan al’amarin ina jin ana ta rade-radi da jita-jita ko ma dai an fada din kai tsaye, a kafofin watsa labarai wasu suna cewa a Bauchi shugabanin majalisar dokokin jihar su biyu ne. ko kadan ba haka zancen yake ba, akwai rafkanuwa da rashin fahimta, sannan akwai wasu ababen da suke fada wadanda ba a tsaya an fetse wa jama’a don su fahimta ba. Shi wannan zaben na Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi da manyan jami’an da suke gudanar da harkokin majalisa ta kowace jiha ce kuwa akwai ka’idodi da matakai da ake dauka da suka jinginu a kan sharuda na gudanar da irin wannan zaben. A Bauchi din an bi sharudan wajen zaben? Bar na ku ji yadda lamarin yake daki-daki. Da farko idan Akawun majalisa ya shigo mambobin majalisar za su shigo su zauna, daga bisani Akawun zai kira Oda na wannan zaman, jama’a za su yi tsit, zai fadi tsarin yadda al’amarin zaman zai kasance. Shi wannan bawan Allah Akawun majalisar ya zauna a ranar Alhamis din da ta gabata ya kira majalisa an zauna ya fadi jadawalin zama da tsare-tsaren abubuwa da wasikar da suka riska daga fadar gwamnatin jihar ta na’am da fara wannan zaman. Bayan ya kammala ya kira sunayen ‘yan majalisun da aka zaba daya bayan daya, mutum 11 kafin a kammala kiran sunan wasu biyu suka shigo saboda haka aka samu mutane 13 a zaune a wannan safiyar. Bayan ya kammala wadannan matakan ya bukaci a dauki matsayin waye zai zama shugaban majalisar jihar (Kakaki), dan majalisa daga jam’iyyar NNPP da ke cikin mazabar Bauchi ba fa jam’iyyar APC ba, NNPP shine ya daga hanu ya ce ya gabatar da sunan Abubakar Sulaiman a matsayin wanda yake jin ya cancanci ya zama shugaban majalisar jihar. Akawun ya tambayi sauran wani dan majalisa ya goyi baya aka kammala zaben nan lami-lafiya, daga karshe sun zabi Abubakar Y.

Sulaiman daga jam’iyyar APC wanda ba dan jam’iyyar PDP, nan take ‘yan uwansa suka masa murna, Akawun majalisar ya rantsar da shi kamar yadda kundun tsarin doka ya tanada, aka zo aka yi zaben Mataimakin shugaban majalisa wanda Dallami Ahmed Kawule ‘yan majalisar suka zaba, aka kuma zabi shugaban masu rinjaye da na marasa rinjaye dukka a wannan zaman.

Daga bisani Kakakin majalisar ya yi jawabinsa har yake cewa ya dage zamar majalisar har zuwa ranar da kuma aka sake zama. Shi kenan zama ta kare domin a daidai lokacin da shugaban majalisa ya yi wannan furicin fa duk wani abu da ke cikin majalisa an tsaida shi kenan domin ya sanya hatimi ya buga.

To a ina aka samu matsalar?

A lokacin da aka tashi za a fita sai ga wasu ‘yan majalisa sun shigo ko da alkairi ko da aka sin haka, amma lokacin da suka shigo bakin alkami ya rigaya ya bushe, saboda haka dukkanin sharuda da dokoki da abun da shari’a ta tanadar kan zaben shugaban majalisar jihar an bisu daya bayan daya kafin a zo a dire a matsayin zaban Abubakar Sulaiman da mataimakinsa Ahmed Kawule.

Babu wata matsala kawai sai wasu ‘yan tsiraru suka kama tsigumi, eh akwai wadanda suka fito daga majalisar suka je jikin inuwar alamar sandar majalisa suka zauna wai yanzu sune ‘yan majalisa za su zabi shugabansu, sai aka samu wani zababben dan majalisa ya fito shine ya tsaya a matsayin Akawun majalisar, sannan aka zabi Akawu, shi kuma ya zo ya ce an zabi Damina abun (Dariya) to ai ko a nan girma ya fadi.

Tun da a wannan tafiyar mun ga yadda rakumi ya durkusa wa ruwar kasko. Babu yadda za ka ce kana shugaban majalisa a wancar marrar kana aiki a cikin wannan majalisar da kujerunsu da ma’aikata da sandar iko da dukanin komai da komai sai aka wayi gari ka fito jikin Lambo jikin bishiya ka ce nan ne majalisar, kun ga an ci mutuncin majalisa an kaskantar da kimar majalisar dokokin jihar Bauchi a idon duniya.

Babu wata dokar da ta ba su damar yin haka ne?

Babu wata doka illa dokar son kai, dokar asha ruwan tsuntsuye ba, amma ba wai dokar da aka sani wacce take a tsarin mulki ba, saboda in ka lura ai wancan bangaren gabaki dayansu ‘yan APC ne, mu kuma a bangaren nan akwai ‘yan APC, NNPP da kuma ‘yan PDP.

Abun da doka ta ce shine ‘yan majalisa idan sun kai sha daya za su yi kaddamar da majalisa da zabe, ba ma wai ‘yan majalisu sha daya muke da su ba, ‘yan majalisu 13 ne, kuma ina tabbatar muku wasu karin ‘yan majalisu za su dawo wannan bangaren ta gaskiya.

Mu yanzu abun da ke gabanmu shine mu ci gaba da harkar gwamnati don ganin cewa jihar Bauchi ta samu mafita daga matsalolin da take ciki da halin kaka na kayi.

Ku a bangaren gwamnati da wasu bangare za ku yi aiki?

Da bangaren mutuntaka bangaren wacce doka ta yi bayani, aka kuma rigaya aka yi, shine zabin Abubakar Sulaiman, saura in suka ce sun shigo sannu a hankali ba mu da matsala da kowa, shi gwamna Sanata Bala Muhammad Abdulkadir tunkaho da demokradiyya kofarsa a bude take ya zo ya zauna da kowa. Kai a bangaren gwamnati kake, wannan kuma hidimace ta majalisa ba

ka ganin jama’a za su ce meye sa ba ku bar majalisar su ci gaba da muhawararsu ba?

Idan kuka lura tun lokacin da wannan batun ya faru mu ba mu ce komai ba sai yanzu, amma abun da nake son ko gane shine ita hidimar yada labarai ba ta iyuwa ba tare da wayar da kan jama’a ba.

Majalisar nan ta jihar Bauchi ce, majalisar nan ba ta da ‘yan jarida da aka nada da za su yi irin wannan aikin kawo yanzu, don haka ne a gwamnatance muka ga gibin ya yi yawa shirun kuma ya yi yawa don haka ne muka ga ya dace mu fahimtar da jama’a hakikanin abun da ya faru.

Eh ni Kakakin gwamnan Bauchi ne amma ba na fito ne don na yi magana a matsayina na Kakakin gwamna ba, a’a ina magana ne a matsayin Kakakin gwamnatin jihar Bauchi, domin kai tsaye wannan lamarin ya shafi gwamnati, domin ita gwamnati daman tana kunshe ne da sashin gwamna da sashin dokokin da kuma sashin shari’a, idan aka samu abu guda da ya fadada dole ne mu fito mu fayyace wa jama’a yadda abu yake faruwa domin jama’a su san cewar babu wata matsala kamar yadda aka yada musu a farko.

Kana ganin wannan abun da ya faru ko yake faruwa akwai wasu da suke kokarin kawo muku tsaiko ne wajen tafiyar da gwamnati ko yaya? Eh to hakan zai iya faruwa domin wani lokacin kana neman wuta ne a makera sai ka tarar da ita a masaka. Wadannan da muke magana suka je suka ce sun yi nasu zaben su Hon.

Kawuwa Damina da mutanensa kun san sune suka soke dokar kwato kadarorin da aka yi almundahana da kudaden gwamnati a lokacin da Kawuwa ke shugaban majalisar jihar ta takwas a watannin da suka gabata, wanda mutum 11 ne suka halllara a wannan zaman, kafin ‘yan uwansu su zo son kammala yin abun da za su yi.

Tsoron kada allura ta tono garma domin masu gidansu suna ganin kamar idan aka bar majalisar ta yi aikinta yadda ya kamata kamar za a fallasa wadanda suka yi awun gaba da dukiyar jama’an jihar da sauransu a’a za a kaisu gidan wakafi ko a je ana tuhumarsu kan wawushe dukiyar jama’a. kada ka dada kada ka kara wadannan dalilan ne ni a ganina ya sa suke wannan abun.

Ina son na shaida maka cewar gwamnatinsa Sanata Bala Muhammad Abdulkadir za ta dauki kudurin kwato dukiyar jama’an jihar Bauchi da aka yi babakere da almundahan da su a hanun kowa waye ko waye kuwa fa.

Takamaimai mene ne ya tayar muku da hankali daga abun da kuka hango ne kam?

Wasu abubuwan kare ba zai ci ba, zan baku misalin guda daya tak, an yi batun cewar gwamnatin da ta gabata ta sayo kayyakin bison mamaci da kudin ya zarce biliyan biyu a cikin wata 5 kacal. naira miliyan dari tara da sittin aka bayar don sayo likkafani a cikin wata fiyar kacal, aka sake kashe biliyan 1.3 don sayo itace (Katakai) da za a rufe mamaci a cikin makabartun jihar Bauchi a cikin wata biyar fa. alhali wannan sam ba harkar gwamnati ba ne amma domin a yi almundahana shine aka ware kudi.

Malam yaushe ne gwamnati za ta kashe sama da biliyan 2 ga wadanda suka rasu amma ba a kashe biliyan uku ga wadanda suke fama da rashin lafiya ba, wasu abubuwan da aka yi a jihar Bauchi a gwamnatin baya wasu sai ka sha mamaki sosai idan ka ji, amma wadannan abubuwan balo-balo haka muka ganosu an yi.

Za ku je gaban wata hukuma don tuhumar hakan ne?

Duk wata hukumar da ta dace za mu je gabanta domin a dawo wa jama’an jihar Bauchi kudadensu da aka wawushe, ina tabbatar wa jama’ar jihar Bauchi cewar sisi da kwabonsu da aka wawushe sai an amayar.

Dukkanin hukumomin da su ka dace za mu je gabansu domin a kwato wadannan kudaden, babu wani sassauci domin idan mu ka yi sassauci Allah zai taimayemu, za mu bi dukkanin matakai wajen kwato kudaden nan dukkanin wata hukumar da ta dace za mu nemota domin ta kwato dukiyar jama’a da wasu tsiraru suka yi wa jihar cin-kaca ba, sai an dawo da kudaden nan domin mu hada mu yi wa jama’a aiki.

Da ana cewa wannan gwamnatin za ta ja layi kan irin wannan batun domin kada tuhume-tuhume ya hanata gudanar da aiyukan da su ke gabanta?

Malam ka ja layi da sanda wani ya zo ya ja maka layi da wuka sai ka tsaya sai ya yanka ka?

Babu yadda za a yi mutum bai bi layin da ya dace a ce kuma a ja layi ba, an ja layin ya yi haka.

@://hausa.leadership.ng

47 thoughts on “Abinda Tawagar Damina Su Ka Yi Cin Mutuncin Majalisar Dokokin Bauchi Ne – Dakta Ladan

Leave a Reply

Your email address will not be published.