APC ta nada sabon sakataren jam’iyya na kasa

Kwamitin gudanarwa na uwar jam’iyyar APC ya amince da nadin Victor Giadom a matsayin sabon mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa.

An nada Giadom ne domin ya maye gurbin tsohon sakataren jam’iyyar, Mai Mala Buni, wanda yanzu shine zababben gwamnan jihar Yobe.

Sanarwar da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya fitar, ta ce Mista Giadom zai kasance sakatare na riko kwarya har zuwa lokacin da jihar Yobe zata fitar da da wanda zai gaji Mista Buni a matsayin sakatare mai cikakken iko.

Kafin nada shi a matsayin sakatare na rikon kwarya, Mista Giadom, wanda dan asalin jihar Ribas ne, shine mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa.

Mista Giadom ya taba zama shugaban karamar hukumar Gokana kafin daga bisani tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan sufuri a yanzu, Rotimi Amaechi, ya nada shi a matsayin kwamishina daga shekarar 2011 zuwa 2015.

@hausa.legit.ng

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *