Ana ci gaba da kai hare-hare a Sri Lanka

Ana ci gaba da samun bayanai na sabbin hare-hare da ake kai wa Sri Lanka.

Wakilin BBC da ke lardin Colombo ya ruwaito cewa an kara samun wani harin bam a wani otel da ke daura da wani gidan zoo inda a kalla mutane biyu suka rasa ransu.

Rahotanni sun bayanna cewa mutum biyu da aka kashe a harin ‘yan sanda ne.

Sai kuma wani sabon hari da aka kai a lardin Dematagoda wanda zuwa hada wannan labarin babu cikakken bayani a kaiTsallake Twitter wallafa daga @AzzamAmeen

2 dead in an explosion took place inside a small hotel in Dehiwela pic.twitter.com/wR5wMinueb— Azzam Ameen (@AzzamAmeen) 21 Afirilu, 2019

Karshen Twitter wallafa daga @AzzamAmeenTsallake Twitter wallafa 2 daga @AzzamAmeen

Another explosion reported from Dematagoda, Colombo. 8th of the day— Azzam Ameen (@AzzamAmeen) 21 Afirilu, 2019

Karshen Twitter wallafa 2 daga @AzzamAmeen

Wadannan su ne hare-hare na takwas da aka kai a ranar Lahadi a coci-coci da kuma otel-otel a Sri Lanka da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 140.

An dai sami rahotannin tashi bama-bamai shida, kuma coci-coci guda uku a Kochchikade da Negombo da kuma Batticaloa ne aka kai wa harin a daidai lokacin da ake bukukuwan Easter.

An kuma kai wa otel din Shangri La da na Cinnamon Grand da kuma na Kingsbury hari, kuma dukkan hare-haren sun auku ne a birnin Colombo.

Sai kuma a yanzu aka kara samun wadannan da ya zama na bakwai na otel din da ke lardin Colombo da kuma na takwas da aka kai a lardin Dematagoda.

Tun a tashin farko bayan kai hare-haren an bayyana cewa kusan mutum 137 ne suka rasa rayukansu, kuma kusan 300 sun samu raunuka

A yanzu haka dai gwamnatin kasar ta saka dokar hana fita sakamakon lamarin da ke kara ta’azzara

Bikin Easter na cikin manyan bukukuwan mabiya addinin Kirista a kasar.

Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda bama baman suka lalata daya daga coci-cocin mai suna St Sebastian’s a birnin Negombo – inda ya yi kaca-kaca da ginin kuma akwai jini ko ina.

Kafafen watsa labarai a kasar na cewa akwai masu yawan bude ido a cikin wadanda harin ya rutsa da su.

@bbc.com/hausa

Abdulazeez Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *